Darussa muhimmaci
1 videyoWudu
3 videyoSalla
3 videyoMühim suallar
272 tambayoyiBANGARAN TAUHIDI42
Tambaya ta: 1. Wanene Ubangijinka?
Amsa - Ubangijina shine Allah wanda ya renenini, kuma ya reni dukkanin halitta da ni'imarsa.
Dalili: Faɗinsa - madaukakin sarki-: (Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai 2). [Suratul Fatiha].
Tambaya ta: 2. Mene ne Addininka?
Amsa - Addini na shine Musulunci, shine: Miƙa wuya ga Allah da Tauhidi, da jawuwa gareshi da biyayya, da kuɓuta daga shirka da ma'abotanta.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Lallai Addini a wajen Allah shine Musulunci}. [Suratul Aal Imran: 19].
Tambaya ta: 3. Wane ne Annabinka?
Amsa: Shine Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Muhammad Manzon Allah ne}. [Suratul Fathi: 29].
Tambaya ta: 4. Ka ambaci kalmar Tauhidi, kuma menene ma'anarta?
Amsa- Kalmar Tauhidi: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" Ma'anarta: Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Ka sani, cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah}. [Suratu Muhammad: 19].
Tambaya ta: 5. A ina Allah - maigirma da ɗaukaka - yake?
Amsa: Allah yana sama, asaman Al'Arshi, a saman dukkanin halittu. Allah - maɗaukain sarki - yace: {Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'Arshi}. [Suratu Daha: 5}. Kuma yace: {Shĩne marinjayi a kan bayinsa, kuma shine Mai hikima, Masani}. [Suratul An'am: 18].
Tambaya ta 6: Menene ma'anar shaidawa cewa lallai Muhammad Manzan Allah ne?
Amsa- Ma'anarta: Lallai cewa Allah ya aiko shi ga dukkanin talikai mai bushara kuma mai gargadi.
Yana wajaba:
1. Yi masa biyayya a dukkanin abinda yayi umarni.
2. Gasgatashi acikin dukkanin abinda ya bada labari.
3. Rashin saɓa masa.
4 Ba'a bautawa Allah sai da abinda ya shar'anta, wannan shine koyi da Sunnah da kuma barin Bidi'a.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Dukkan wanda yabi Manzo to haƙiƙa yabi Allah} [Al-Nisa'i: 80], Kuma - tsarki ya tabbatar masa - yace: {Kuma ba ya furuci daga san zuciya, shi bai zamoba, sai wahayi ne da akeyi masa 4}. [Suratu Al-Najmi: 3-4]. Kuma Allah - mai girma da ɗaukaka - yace: {Haƙiƙa koyi kyakykyawa ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã ƙaunar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa 21}. [Suratu Al-Ahzab: 21].
Tambaya ta: 7 Saboda me Allah - maɗaukakin sarki - ya halicce mu?
Amsa- Ya halicce mu ne dan bauta masa shi kaɗai ba shi da abokin tarayya.
Badan wargiba ko wasa.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Kuma ban halicci Aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta mini 56}. [Suratu Al-Zariyati: 56].
Tambaya ta:8. Mecece Bauta?
Amsa- Ita suna ne mai tattarowa ga dukkanin wani abin da Allah yake sonsa, kuma ya yarda dashi daga maganganu da ayyuka na ɓoye dana bayyane.
Na bayya ne: Kamar ambaton Allah da harshe daga Tasbihi da godewa, Allah da yin Kabbara da sallah da Hajji.
Na ɓoye: Kamar dogaro ga Allah, da tsoro, da ƙauna.
Tambaya:9 Menene mafi girman wajibi akan mu?
Amsa- Mafi girman wajibi akammu shine: Kaɗaita Allah - maɗaukakin sarki -.
Tambaya ta: 10.Mene ne nau'ukan Tauhidi?
Amsa- 1. Tuhidi na Rububiyyah: Shine imani da cewa Allah shine Mahalicci, Mai azurtawa, Mamallaki Mai juya al'amura, shi kaɗai yake, bashi da abokin tarayya.
2. Tuhidi na Uluhiyya: Shine kaɗaita Allah da bauta, baza'a bautawa wani ɗaya ba sai Allah - maɗaukakin sarki -.
3. Tauhidi na Sunaye da Siffofi: Shine yin imani da dukkanin sunaye da siffofi na Allah - maɗaukakin sarki - waɗanda sukazo acikin littafi da Sunna, batare da misaltawa, ko kamantawa ko korewa ba.
Dalilin Nau'ukan tauhidi guda uku: Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Shine Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, to sai ka bauta masa, kuma kayi haƙuri ga bautarsa. Shin kã san wani takwara gareshi 65}. [Suratu Maryam: 65].
Tambata ta 11. Mene ne mafi girman zunubi?
Amsa- Shirka da Allah - maɗaukikin sarki -.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Lalle Allah baya gãfarta ayi shirki dashi, kuma yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda yake so, kuma wanda yayi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma 48}. [Suratu Al-Nisa'i: 48].
Tambaya ta 12. Ka ambaci shirka da nau'ukanta.
Amsa- Shirka: Itace juyar da kowane nau'i daga cikin nau'ikan ibada ga wanin Allah - maɗaukakin sarki -.
Nau'ukanta:
Babbar shirka, Misali: Kiran wanin Allah - maɗaukakin sarki -(kira na bauta) ko yin sujjada ga wanin Allah - tsarki ya tabbatar masa - ko kuma yanka ga wanin Allah - mai girma da ɗaukaka -.
Karamar Shirka, misali: Rantsuwa da wanin Allah - maɗaukakin sarki -,ko layu, shine abinda ake ratayawa daga abubuwa dan jawo wani amfani, ko tunkuɗe wata cuta, da sassauƙan riya, kamar ya kyautata sallarsa dan abinda yake gani daga kallon mutane zuwa gareshi.
Tambaya 13. Shin wani ɗaya wanda ba Allah ba ya san gaibu?
Amsa- Babu wani wanda yasan gaibu sai Allah shi kaɗai.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Kace bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su 65}. [Suratu Al-Naml: 65].
Tambaya ta 14. Lissafa rukunan Imani.
Amsa- 1. Imani da Allah - maɗaukakin sarki -.
2. Da Mala'ikun sa.
3. Da Littatafan sa.
4. Da Manzannin sa.
5. Da ranar ƙarshe.
6 Da Kaddara alherinsa da kuma sharrinsa.
Dalili: Shine Hadisin nan shahararre na Jibrilu, a wajen Muslim, Jibrilu yacewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -: "Kabani labari game da imani, yace: Kayi Imani da Allah, da Mala’ikunsa, da littattafansa, da Manzanninsa, da ranar Lahira, kuma kayi imani da ƙaddara alherinsa da sharrinsa".
Tambaya ta 15. Kayiwa rukunan imani sharhi.
Amsa: Imani da Allah.
Ka yi imani da cewa Allah shi ne wanda ya halicceka kuma ya azurtaka, shine kuma mamallakin halittu mai jujjuya lamuran halittu shi kaɗai.
Shine kuma abin bautawa, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai shi.
Kuma shi ne mai cikakken girma, wanda yake dukkan godiya ta tabbata gareshi, kuma shi ke da sunaye kyawawa da kuma siffofi maɗaukaka, bashi da abokin tarayya, kuma wani abu baiyi kama dashi ba, tsarki ya tabbatar masa.
Imani da Mala'iku:
Sune ababen halittar da Allah ya halicce su daga harske,kuma domin bautarsa, da cikakken jawuwa ga umarninsa.
Daga cikinsu akwai Jibrilu - amincin Allah ya tabbata agareshi - wanda yake saukar da wahayi ga Annabawa.
Imani da Litattafai:
Sune littattafan da Allah ya saukar da su ga Manzanninsa.
- Kamar Al-ƙur'ani: Ga Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
- Injila: Ga Annabi Isa - amincin Allah ya tabbata agareshi -.
- Attaura ga Annabi Musa - amincin Allah ya tabbata agareshi -.
- Zabura ga Annabi Dawud - amincin Allah ya tabbata agareshi -.
- Takardun Annabi Ibrahim da Annabi Musa; Ga Ibrahim da Musa.
Imani da Manzanni:
Sune waɗanda Allah ya aiko su zuwa ga bayinsa, domin su ilmantar dasu, kuma suyi musu bushara da alheri da Aljanna, su kuma yi musu gargaɗi da sharri da kuma wuta.
- Mafifitansu: Sune Ulul Azmi, sune:
Annabi Nuhu - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Ibrahim - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Musa - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Isa - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Imani da Ranar Lahira:
Shine abinda yake bayan mutuwa, a ƙabari, da ranar Al-ƙiyama, ranar tashi daga ƙabari, da hisabi, yadda 'yan Aljanna zasu tabbata acikin masaukansu, da 'yan wuta acikin masaukansu.
Imani da ƙaddara alherinsa da kuma sharrinsa:
Kaddara: Shine ƙudurcewa a zuciya cewa Allah yana sanin dukkan wani abu da yake kasancewa a kasantattu, kuma cewa shi ya rubuta wannan abin acikin Lauhul Mahfuz, kuma yaso samuwarsa da kuma halittarsa.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Lalle ne mu kowanne abu mun halicce shi da ƙaddara 49}, [Suratu Al-kamar: 49].
- Shi yana kan matakai huɗu:
Na ɗaya: Sanin Allah - maɗaukakin sarki - yana daga wannan saninsa wanda ya rigayi dukkan komai, kafin afkuwar abubuwa da bayan afkuwarsu.
Dalilinsu: faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Lalle Allah a wurinsane kawai sanin Al-ƙiyama, kuma yanã saukar da girgije, kuma yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai, kuma wani rai bai san abin da zai aikatãba a gõbe, kuma wani rai bai san a wace ƙasã zai mutuba. Lalle Allah Masani ne Mai bada labari 34}. [Suratu Luƙman: 34].
Na biyu: Cewar Lallai ya rubuta wannan a Lauhul Mahfuz, dukkan wani abu da ya kasance, da kuma zai kasance to a rubuce yake a wurin Allah a cikin littafi.
Dalilinta: Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Kuma a wurinSa mabũɗan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce shi, kuma yanã sanin abin da ke a cikin sarari da kogi, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa 59}. [Suratu Al-An'am: 59].
Na Uku: Shine kowannce abu da yake faruwa da ganin damar Allah ne, babu wani abu dazai faru daga gare shi ko kuma daga halittarsa sai da ganin damarsa - maɗaukakn sarki -.
Dalilinta: Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Ga wanda yaso daga cikinku to ya tsaya kan tafarki madaidaici 28 kuma ba komai kuke nufin aikatawa ba sai in Allah ya so, shine Ubangijin talikai}. [Suratu Al-Takwir: 28,29].
Na huɗu: Imani da cewar dukkanin kasantattu ababen halittane Allah ya haliccesu, kuma ya halicci zatinansu da siffofnsu da motsinsu, da dukkanin wani abu acikinsu.
Dalilinta: Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Allah ne ya halitta ku da abin da kuke aikatãwa 96}. [Suratu Al-Saffat: 96].
Tambaya ta: 16. Menene ma'anar Al-ƙur'ani?
Amsa- Shine Zancan Allah - maɗaukakin sarki - wanda ba abin halitta bane.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Idan wani ɗaya daga mushirikai ya nemi tsarinka to, ka tsareshi har sai yaji zancen Allah}. [Surat Al-Taubah: 6].
Tambaya ta: 17. Mecece Sunnah?
Amsa- Itace dukkan wata magana ko aiki ko tabbatarwa ko siffar halitta ko kuma siffar halayya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Tambaya ta: 18. Mece ce Bidi'a? shin za mu iya karɓarta?
Amsa- Dukkanin abinda mutane suka ƙirƙira acikin Addini, wanda bai kasance a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - da kuma sahabbansa ba.
Bazamu karɓi bidi'a ba, kuma zamu mayar da ita ne.
Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin su tabbata agareshi -: "Dukkanin Bidi'a ɓata ce". Abu Daud ya ruwaito shi.
Misalin::Kari a Ibada, kamar ƙara wanki na huɗu a lwala, kamar taron Mauludi, wannan bai zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbansa ba.
Tambaya: 19. ka ambaci Aƙidar Jiɓintarwa da barranta.
Amsa- Jiɓintarwa: Shine son muminai da kuma taimaka musu.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Muminai maza da muminai mata sashinsu masoyan sashine}. [Surat Al-Taubah: 71].
Barranta: Shine ƙin kafirai da kuma adawa dasu.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Haƙiƙa koyi kaykaykyawa gareku ya kasance ga Ibrahim da waɗanda suke tare da shi, a lokacin da suka cewa mutanensu lallai mu masu kuɓutane daga gareku da abinda kuke bautawa wanin Allah mun kafirce muku, adawa da gaba ta bayyana atsakaninmu da tsakaninku har abada har sai kunyi imani da Allah shi kaɗai}. [Suratu Al-Mumtahanah: 4].
Tambaya ta 20. Shin Allah zai karɓi wanin musulunci a matsayin Addini?
Amsa- Allah ba zai karɓi wanin Addinin musulunci ba.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Duk wanda ya nemi wanin musulunci amatsayn Addini to ba za'a karɓa daga gareshi ba kuma a lahira yana daga masu asara 85}. [Surat Aal Imran: 85].
Tambaya ta: 21. Kafirci yana kasancewa da magana da kuma aiki da ƙudurin zuci, ka bada misali ga haka?
Amsa- Misalin magana: Zagin Allah - tsarki ya tabbatar masa -, ko Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Misalin aiki: Wulaƙantar da Al-ƙur'ani ko sujjada ga wanin Allah - maɗaukakin sarki -.
Misalin ƙudurin zuciya: Shine ƙudurce cewa akwai wani da ya cancanci ibada wanda ba Allah - maɗaukakin sarki - ba, ko kuma cewa anan akwai wani mahalicci tare da Allah - maɗaukakin sarki -.
Tambaya ta: 22. Menene munafinci da nau'o'insa?
Amsa:
1- Babban Munafunci: Shine ɓoye kafirci da kuma bayyanar da imani.
Yana fitarwa daga musulunci, kuma shi yana daga kafirci mafi girma.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Lalle munafikai suna can ƙasan ƙasa na wuta, kuma ba zaka taɓa samar musu mataimaki ba}. [Surat Al-Nisa'i: 145].
2.Karamin munafunci:
Misalin: Karya, saɓa alkawari, da cin amana.
Wannan ba ya fitarwa daga musulunci, shi yana daga cikin zunubai, kuma maiyin shi abin bijirowane ga azaba.
Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Alamomin munafuki uku ne: Idan yai zance sai yayi ƙarya, idan yayi alƙawari sai ya saɓa, kuma idan aka amince masa sai yayi ha'inci". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Tambaya ta: 23. Wanene cikamakin Annabwa da Manzanni?
Amsa: Shine Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, sa dai Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabãwa}. [Surat Al-Ahzab: 40]. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Nine cikamakin Annabawa babu wani Annabi baya na". Abu Daud da Tirmizi da Nasa'i da wasunsu ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta: 24. Mece ce Mu'ujiza?
Amsa- Mu'ujiza itace: Dukkanin abinda Allah ya badashi ga Annabawansa na abubuwan da suka saɓa al'adu domin shiryarwa akan gaskiyar su, misali:
-Tsagewar wata ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
- Tsagewar kogi ga Annabi Musa - amincin Allah ya tabbata agareshi - da kuma nitsar da Fir'auna da rundunarsa.
Tambaya ta: 25. Suwaye Sahabbai? Shin ina son su?
Amsa- Sahabi: Shne dukkan wanda ya haɗu da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yana mai imani dashi, kuma ya mutu akan musulunci.
- Muna son su, muna koyi dasu, kuma sune mafi alheri kuma mafifitan mutane bayan Annabawa.
Mafifitansu: Sune halifofi huɗu:
Abubakar - Allah ya yarda dashi -.
Umar - Allah ya yarda dashi -.
Usman - Allah ya yarda dashi -.
Aliyu - Allah ya yarda dashi -.
Tambaya ta 26. Suwaye uwayan muminai?
Amsa: Sune matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Allah - Maɗaukakin sarki yace: {Annabi shine mafi cancanta ga muminai ga kansu, kuma matansa uwayansu ne}. [Surat Al-Ahzab: 6].
Tambaya ta: 27. Menene haƙƙin iyalan gidan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - akanmu?
Amsa: Muna sonsu, muna jiɓintarsu, kuma muna ƙin duk wanda yake ƙinsu, bama wuce gona da iri akansu, sune matansa, da zuriyarsa, da 'Ya'yan Hashim da 'Ya'yan Muɗallab daga muminai.
Tambaya ta: 28. Menene wajibinmu dangane da majiɓinta al'amuran musulmai?
Amsa: Wajibinmu: Shine girmamasu da ji da biyayya garesu a duk abinda ba saɓoba, da barin yi musu tawaye, da yi musu addu'a da yi musu nasiha a sirrance.
Tambaya ta: 29. Wannene gidan muminai?
Amsa: Aljanna. Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Lalle ne Allah Yanã shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu}. [Surat Muhammad: 12].
Tambaya ta: 30. Wannene gidan kafirai?
Amsa: Wuta, Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Ku ji tsoron wuta wacce makamashinta mutane da duwatsu an tanadeta ga kafirai 24}. [Surat Al-Baƙarah: 24].
Tambaya ta: 31.Menene tsoro?, kuma menene ƙauna? Menene dalili?
Amsa:Tsoro, shine jin tsoron Allah da kuma uƙubarsa.
Kwadayi: Shine kwaɗayin ladan Allah da gafararsa, da kuma rahamarsa.
Dalili: Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Waɗancan, waɗanda suke kiran, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanci? Kuma sunã kwadayin sãmun rahamarsa, kuma sunã tsõron azãbarsa. Lalla ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce 57}. [Surat Al-Isra'i: 57]. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - yace: {Ka bawa bayina labari, lalle nine Mai yawan gafarane, kuma Mai yawan jinƙaine 49. Kuma lallai azabata itace azaba mai raɗaɗi 50}. [Surat Al-Hujrat: 49-50].
Tambaya ta: 32. Ambaci wasu daga cikin sunaye da siffofin Allah - maɗaukakin sarki -.
Amsa- Allahu, Ubangiji, Mai yawan rahama, Mai yawan ji, Mai yawan gani, Mai yawan sani, Mai yawan azirtawa, Rayayye, Mai girma, zuwa wanin wannan na abinda ya shafi sunaye kyawawa da kuma siffofi maɗaukaka.
Tambaya ta: 33. Kayiwa waɗannan sunayen sharhi?
Amsa: ALLAHU, Ma'anarsa Allah abin bautawa da gaskiya, shi kaɗai yake bashi da abokin tarayya.
ARRABBU: Wato Mahalicci Mamallaki Mai yawan azurtawa, Mai jujjuya al'amura, shi kaɗai yake tsarki ya tabbatar masa.
ASSAMI'U: Wanda jinsa ya yalwaci kowanne abu, kuma yana jin dukkanin muryoyi akan saɓaninsu, da karkasuwarsu.
ALBASIRU: Wanda yake ganin kowanne abu, kuma yana ganin komai ya ƙaranta ko ya girmama.
AL'ALIMU: Shine wanda iliminsa ya kewaye kowanne abu, wanda ya wuce, dana yanzu, da kuma na nan gaba.
ARRAHMAN: Wanda ramhamarsa ta yawalci dukkanin abin halitta da kuma rayayye, dukkanin bayi da sauran ababen halitta suna ƙarƙashin rahamarsa ne.
ARRAZZAKU: Wanda agareshi ne arziƙin dukkanin halittu yake, daga mutane da Aljanu da sauran dukkanin dabbobi.
ALHAYYU: Shine Rayayye wanda baya mutuwa, kuma dukkanin halitta zasu mutu.
AL'AZIMU: Wanda yake da kamala da girma dukkaninsu, a sunayansa da siffofinsa da kuma ayyukansa.
Tambaya ta: 34. Menene wajibinmu dangane da malaman musulmai?
Amsa- Musosu, kuma mu koma zuwa garesu acikin mas'aloli da abubuwan shari'a masu sauka, kada mu ambacesu sai da kyakkyawan abu, wanda ya ambacesu bada wannan ba, daga mummunan abu to wannan ba akan hanya yake ba.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Allah yana ɗaga darajojin waɗanda suka yi imani daga gareku, da waɗanda aka basu ilimi, Allah Mai bada labarine game da abinda kuke aikatawa 11}. [Surat Al-Mujadalah: 11].
Tambaya: 35. Suwaye waliyyan Allah - maɗaukakin sarki -?
Amsa- Sune muminai masu tsoron Allah.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Ku saurara, Lalle ne masõyan Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bãzãsu kasance sunã yin baƙin ciki ba 62. Sune wadanda sukayi imani kuma sun kasance suna jin tsoron Allah 63}. [Surat Yunus: 62-63].
Tambaya ta: 36. Shin imani faɗa ne da kuma aikatawa?
Amsa- Imani faɗa ne, da aikatawa da kuma ƙudurin zuciya.
Tambaya ta: 37. Shin imani yana ƙaruwa kuma yana raguwa?
Amsa- Imani yana ƙaruwa da biyayya, kuma yana raguwa da saɓo.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Abin sani kawai, mũminai sũne waɗanda suke idan an ambaci Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinsa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãnin, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara 2}. [Surat Al-Anfal: 2].
Tambaya ta: 38. Menene kyautatawa?
Amsa- Shine ka bautawa Allah kamar kana ganinsa, idan baka kasance kana ganinsa ba, to shi yana ganinka.
Tambaya ta: 39. Yaushe ayyuka zasu zama karɓaɓɓu a wurin Allah?
Amsa- Da sharuɗɗa guda biyu:
1. Idan sun zama da tsarkakakkiyar niyya kuma saboda Allah -maɗaukakin sarki - ne.
2. Idan sun kasance akan karantarwar Annabi - tsira da amincin Alla su tabbata agareshi - ne.
Tambaya ta: 40. Menene dogaro ga Allah - maɗaukakin sarki -?
Amsa- Shine dogara ga Allah - maɗaukakin sarki - akan dukkanin abinda zai janyo anfaninnika da tunkuɗe cututtuka, tare da riƙo da sabubba.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Wanda ya dogara ga Allah to shi ya isar masa}. [Surat Al-Dalaƙ: 3].
Ma'anar: {HASBUHU}: Wato ya isar masa.
Tambaya ta:41. Menene wajibin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi?
Amsa- Aikin alheri: Shine horo da dukkan biyayya ga Allah - maɗaukakin sarki -, abin ƙi kuma: Shine hani daga dukkanin saɓawa Allah - mai girma da ɗaukaka -.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Kun kasance mafificiyar al'umma da aka fitar da ita ga mutane, kuna horo da aikin alheri, kuma kuna hani daga abin ƙi, kuma kuna yin imani da Allah}. [Surat Aal-Imran: 110].
Tambaya ta: 42. Suwaye Ahlussunnah wal Jama'ah?
Amsa- Sune waɗanda suka kasance a kan irin abinda Annabi - tsira da amincin Alla su tabbata agareshi - da sahabbansa suka kasance akansa, acikin faɗa da aiki da ƙudirin zuciya.
An ambacesu da Ahlussunna ne: Saboda binsu sunnar Annabi - tsira da amincin Alla su tabbata agareshi - da kuma barin ƙirƙira.
Waljama'a: Domin cewasu sun haɗu akan gaskiya basu rarrabu acikintaba.
BANGAREN FIQIHU.47
Tambaya ta: 1. Kafaɗi ma'anar tsarki?
Amsa- Tsarki: Shine ɗauke kari, da kuma kawar da dauɗa.
Tsarkin dauɗa: Shine muslmi ya kawar da dukkan abinda ya afku na najasa akan jikinsa, ko akan tufafinsa, ko akan bigire da wurin da zai yi sallah acikinsa.
Tsarkin kari: Shine wanda yake kasancewa a alwala ko wanka, da ruwa mai tsarkakewa, ko kuma taimama ga wanda ya rasa ruwa, ko kuma amfani da ruwan ya wuyata akansa.
Tambaya ta: 2. Ya zaka tsarkake abinda najasa ta sameshi?
Amsa- Ta hanyar wankeshi da ruwa har sai ya tsarkaka.
- Amma abinda kare yayi lallagi dashi, sai a wankeshi sau bakwai, na farkon da ƙasa.
Tambaya ta: 3. Menene falalar Alwala?
Amsa- Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - yace: "Idan bawa musulmi yayi alwala", ko kuma "Mumini", "sai ya wanke fuskarsa, to kowane kuskure zai fita daga fuskarsa da yayi duba zuwa gareshi da idanuwansa tare da ruwan", ko kuma "Tare da ƙarshen ɗigon ruwan", "Idan ya wanke hannayensa, kowane kuskure zai fita daga hannayensa waɗanda hannayensa suka damƙa dasu tare da ruwan" ko "Tare da ƙarshen ɗigon ruwan", "Idan ya wanke kafafuwansa kowane kuskuren da ƙafafuwansa suka tafi garesu zasu fita tare da ruwa ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan" "Har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai". Muslim ne ya rawaitoshi.
Tambaya ta: 4. Yaya zakayi alwala?
Amsa: Ka wanke tafuka sau uku.
Sai kayi kuskurar baki ka shaƙa ruwa, ka kuma face sau uku.
Kuskurar baki: Shine sanya ruwa a baki, da kuma karkaɗa shi, da zubar dashi.
Shaƙa ruwa: Shine: Jan ruwa ne ta iska zuwa cikin hanci da hannun damansa.
Facewa: Shine fitar da ruwa daga hanci bayan shaƙawa, da hannun hagunsa.
Sannan wanke fuska sau uku.
Sannan wanke hannuwa biyu zuwa gwiwar hannu sau uku.
Sannan shafar kai, zaka fuskanto da hannayenka sannan kayi baya, sai ka shafi kunnuwa biyu.
Sannan ka wanke ƙafafuwanka biyu zuwa idan sawu sau uku.
Wannan shine mafi cika, haƙiƙa wannan ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Alla su tabbata agareshi - acikn hadisai acikin Bukhari da Muslim, waɗanda Usman da Abdullahi ɗan Zaid da wasunsu suka ruwaitosu. Kuma haƙiƙa ya tabbata a Bukhari da waninsa: "Lallai cewa shi yayi alwala sau ɗai-ɗai, kuma cewa shi yayi alwala sau biyu-biyu", ma'ana: Lallai cewa shi yana wanke kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwala sau ɗai-ɗai, ko sau biyu-biyu.
Tambaya ta 5. Menene farillan alwala, kuma ka lissafa su?
Amsa- Sune waɗanda alwalar musulmi bata inganta idan yabar ɗaya daga cikinsu.
1. Wanke fuska, daga gareshi akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa.
2. Wanke hannuwa biyu zuwa gwiwar hannaye biyu.
3. Shafar kai, daga gareshi akwai kunnuwa biyu.
4. Wanke ƙafafuwa biyu zuwa idon sawu biyu.
5. Jerantawa tsakanin gaɓɓai, ta yadda zai wanke fuska, sannan hannuwa biyu, sannan shafar kai, sannan wanke ƙafafuwa biyu.
6.Bibiya: Shine yin alwala a lokaci guda abin sadarwa, ba tare da rabawa ga lokacinba, har sai gaɓɓai sun bushe daga ruwa.
- Kamar yayi rabin alwalar, sai yacike ragowar awani lokacin daban, to alwalarsa bata ingantaba.
Tambaya ta 6. Menene sunnonin alwala, kuma ka lissafa su?
Amsa- Sunnonin alwala: Sune waɗanda da zai aikatasu to yana da ƙari na lada da sakamako, da zai barsu, to babu laifi akansa, kuma alwalarsa ingantacciyace.
1. Ambaton Allah: Bismillah.
2. Yin asuwaki.
3. Wanke tafukan hannu biyu.
4. Tsettsefe yatsu.
5. Wankewa na biyu da na uku ga gaɓɓai.
6. Farawa da dama.
7. Yin zikiri bayan alwala: "Ina shida cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai yake, bashi da abokin tarayya, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzonsane".
8. Yin sallah raka'a biyu bayanta.
Tambaya ta 7. Ka lissafa masu warware alwala.
Amsa- Abinda ya fita ta mafita guda biyu; gaban mutum da dubura, na fitsari da bayan gida da tusa.
Bacci, ko hauka, ko kuma suma.
Cin naman raƙumi.
Shafar gaba ko dubura da hannu ba tare da shamaki ba.
Tambayata: 8. Mecece Taimama?
Amsa- Taimama: Itace amfani da turɓaya ko waninta daga bigiren ƙasa, yayin rasa ruwa, ko kuma wuyatar yin amfani dashi.
Tambaya ta 9: Ya zakayi Taimama?
Amsa- Bugun kasa bugu ɗaya da cikin tafikan hannaye biyu, da shafar fuska, da bayan tafukan hannaye biyu sau ɗaya.
Tambaya ta: 10. Suwaye masu ɓata Taimama?
Amsa- Dukkan masu ɓata alwala.
Idan aka sami ruwa.
Tambaya ta: 11, Menene huffi biyu da safa? shin za a iya yin shafa akansu ?
Amsa- Huffina biyu: Sune abinda ake sakawa a ƙafa na fata.
Safuna biyu: Sune abinda ake sakawa a ƙafa waɗanda bana fata ba.
An halatta yin shafa akansu maimakon wanke ƙafafuwa biyu.
Tambaya ta: 12. Ka ambaci hikima daga shafa akan huffi biyu.
Amsa- Sauƙaƙawa da rangwami ga bayi, musamman acikin lokutan sanyi da ɗari da halin tafiya, ta yadda cire abinda ke cikin ƙafafuwa yake wahala.
Tambaya: 13. Menene sharuɗɗan ingancin shafa akan huffi?
Amsa- 1. Ya sanya huffi biyun akan tsarki, wato bayan alwala.
2. Huffin ya zama mai tsarki, shafa akan najasa bata halatta.
3. Huffin ya kasance mai rufewa ga wuri abin wajabta wankeshi acikin alwala.
4. Shafar takasance acikin mudda abar iyakancewa, ga mazaunin gida ba matafiyiba: Yini ɗaya da dare, matafiyi kuma: Kwana uku da dararensu.
Tambaya: 14. Mecece siffar shafa akan huffi?
Amsa- Siffar shafar itace: Ya sanya yatsun hannyensa biyu masu danshi da ruwa akan yatsun ƙafafuwansa biyu, sannan sai ya tafi dasu zuwa ƙwaurinsa, yana shafar ƙafar dama da hannun dama, ƙafar hagu da hannun hagu, zai kuma ware yatsunsa idan yayi shafar, kada ya maimaita.
Tambaya: 15. Menene yake warware shafa akan huffi?
Amsa- 1. Karewar kwanakin shafar, shafa akan huffi baya halatta bayan ƙarewar muddar shafar abar iyakancewa a shari'ah, yini da dare, ga mazaunin gari, da kwanaki uku da dararensu ga matafiyi.
2. Cire huffin biyu, idan mutum ya cire huffin biyu ko ɗayansu bayan shafarsa, to shafar akansu ta ɓaci.
Tambaya ta: 16. Mecece ma'anar Sallah?
Amsa- Sallah: Itace bautawa Allah da wasu maganganu da kuma wasu ayyuka keɓantattu, abar buɗewa da kabbara, abar rufewa sallama.
Tambaya ta: 17. Menene hukuncin sallah?
Amsa- Sallah wajibice akan kowanne musulmi.
Allah - maɗaukakin sark - yace: {Lallai Sallah ta kasance akan muminai farillace mai ƙayyadajjen lokaci 103}. [Surat Al-Nisa'i: 103].
Tambaya ta: 18. Menene hukuncin barin sallah?
Amsa: Barin sallah kafircine, Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - yace:
"Alƙawari a tsakaninmu dasu shine sallah, wanda ya barta to ya kafirta".
Ahmad da Timizi ne da wasunsu suka ruwaitoshi.
Tambaya ta: 19. Salloli nawane suka wajaba akan musulmi a yini da dare ? Sannan nawa ne adadin raka'oin kowacce sallah?
Amsa- Salloli biyar ne a yini da dare, Sallar Asubah: Raka'oi biyu ce, da sallar Azahar: Raka'oi huɗu ce, da sallar La'asar: Raka'oi huɗu ce, da sallar Magariba: Raka'oi uku ce, da sallar Isha'i: Raka'oi huɗu ce.
Tambaya ta 20: Ka lissafa sharuɗɗan sallah?
Amsa: 1. Musulunci, bata inganta daga kafiri.
2.Hankali,bata inganta daga mahaukaci.
3. Wayo, bata inganta daga ƙaramin yaron da bashi da wayo.
4. Niyyah.
5. Shigar lokaci.
6. Tsarki acikin ɗauke hadasi.
7. Tsarkaka daga najasa.
8. Suturce al'aura.
9.Fuskantar Al-ƙiblah.
Tambaya ta 21: Ka lissafa rukunan sallah.
Amsa; Su rukunai goma sha huɗu ne, kamar yanda yake zuwa:
Na farkonsu: Tsayuwa acikin farilla ga mai iko.
Kabbarar Harama, itace: "Allahu Akbar".
Karatun Fatiha.
Ruku'u, sai ya miƙar da gadon bayansa adaidaice, ya kuma sanya kansa daidai da dashi.
Dagowa daga gareshi.
Daidaituwa alhali yana a tsaye.
Sujjada, da kuma tabbatar da goshinsa, da hancinsa, da tafukan hannayensa biyu, da gwiwowinsa biyu, da yatsun gefan diga-digansa daga awurin sujjadarsa.
Dagowa daga sujjada.
Zama tsakanin sujjada biyu.
Sunna: Shine ya zauna yan mai shinfiɗa akan kafarsa ta hagu, yana kuma kafe kafarsa ta dama, yana mai fuskantar da ita zuwa Al-ƙiblah.
Nutsuwa, itace natsuwa akowane rukuni na aiki.
Tahiyar ƙarshe.
Zama domin shi.
Sallama biyu, shine yace sau biyu: "Assalamu alaikum wa rahmatullah".
Jeranta rukunai - kamar yadda muka ambata -, da zaiyi sujjada a misali kafin ruku'insa da gangan to ta ɓaci, idan kuma da rafkannuwane, to dawowa ya lazimceshi dan yayi ruku'u, sannan yayi sujjada.
Tambaya ta 22. Ka ambaci wajiban sallah.
Amsa- Wajiban sallah, su takwas ne, kamar yanda ke tafe:
I. Kabarbari, banda kabbarar Harama.
2. Faɗin: "Sami'Allahu Liman Hamidahu" ga liman damai sallah shi kaɗai.
3. Faɗin: "Rabbana walakal hamdu".
4. Faɗin: "Subhana Rabbiyal Azim", sau ɗaya acikin ruku'i.
5. Faɗin: "Subhana Rabbiyal A'alah", sau ɗaya acikin sujjada.
6.Faɗin: "Rabbighirli", tsakanin sujjada biyu.
7. Tahiyar farko.
8. Zama domin Tahiyar farko.
Tambaya ta 23. Waɗanne ne sunnonin sallah?
Amsa- Goma shaɗaya ne, kamar yanda yake tafe:
1.Faɗinsa bayan kabbarar Harama: "Subhanakallahumma, wabi hamdika, watabarakasmuka, wa ta'ala jadduka, wa la ilaha ghairuka". Ana ambatanta: Addu'ar buɗe sallah.
2. Neman tsari.
3. Yin Bisimillah.
4. Faɗin: Amin.
5.Karatun surah bayan fatiha.
6. Bayyanar da karatu ga liman.
7.Faɗin: "Mil'us samawati, wamil'ul ardhi, wa mil'u ma shi'ita min shai'in ba'adu". Bayan kammala Tahamidi.
8. Abinda yaƙaru akan ɗaya na Tasbihin ruku'i, wato: Tasbihi na biyu da na uku da abinda ya ƙaru akan haka.
9. Abinda ya ƙaru akan ɗaya a tasbihin sujjada.
10. Abinda ya ƙaru akan ɗaya a faɗinsa: "Rabbig firli" Tsakanin sujjada biyu.
11.Yin salati a tahiyar ƙarshe ga iyalansa - tsiran da amici ya tabbata agaresu -, da albarka a gareshi da kuma su, da yin addu'a bayansa.
Na huɗu: Sunnoni na ayyuka, ana ambatansu Al-Hai'at.
1. Daga hannu tare da kabbarar Harama.
2. Da yayin yin ruku'u.
3. Da kuma lokacin ɗagowa daga ruku'in.
4. Da sakko dasu bayan hakan.
5. Dora hannun dama akan na hagu.
6. Dubansa zuwa bigiren sujjadarsa.
7. Warawarsa tsakanin diga-digansa biyu alhali yana tsaye.
8. Damƙar gwiwowinsa da hannayensa, yana mai wara yatsun hannaye a ruku'insa, da kuma miƙar da gadon bayansa acikinsa, da sanya kansa daura dashi.
9. Tabbatar da gaɓuɓuwan sujjada a ƙasa, da kuma damƙar ƙasar ga bigiren sujjada.
10. Buɗa damatsansa ga gefunansa biyu, da kuma raba cikinsa ga cinyoyinsa, da raba cinyoyinsa ga ƙwaurikansa, da rabawarsa tsakanin gwiwowinsa, da tsayar da diga-digansa, da sanya cikin yatsunsu akan ƙasa yana mai rabawa, da sanya hannuwansa daura da kafaɗunsa a shinfide, yatsun kuma a dunƙule.
11. zaman Iftirashi a zama tsakanin sudda biyu, da a zaman Tahiya na farko, da kuma zaman Tawarruk a zama na biyu.
12. Dora hannaye akan cinyoyi suna a shinfiɗe, yatsun a dunƙule tsakanin sujjadu biyu, haka kuma a Tahiya, sai dai cewa shi anan zai damƙi daga ƙaramin ɗan yatsa na gefe dama da mai binsa, yakuma naɗe babban yatsa tare da na tsakiya, yana mai nuni da manuniyarsu yayin ambaton Allah.
13. Juyawarsa dama da hagu acikin sallamarsa.
Tambaya 24: Ka Lissafa abubuwan da suke ɓata sallah?
Amsa-1. Barin wani rukuni ko sharaɗi daga sharuɗɗan sallah.
2. Yin magana da gangan.
3. Ci ko sha.
4. Motsi mai yawa a jere.
5. Barin wani wajibi ɗaya daga cikin wajibabbun sallah da gangan.
Tambata ta: 25. Yaya musulmi zaiyi sallah?
Amsa: Siffar yadda ake sallah.
1.Ya fuskanci Al-ƙibla da dukkanin jiknsa, batare da karkacewaba, ko kuma waiwaye.
2. Sannan yayi niyyar sallar da yake son ya sallaceta a zuciyarsa ba tare da furta niyyar ba.
3. Sannan yayi kabbarar Harama, sai yace: (Allahu Akbar), ya ɗaga hannayensa biyu zuwa daidai da kafaɗunsa biyu yayin kabbarar.
4. Sannan yaɗora tafin hannunsa na dama a bayan tafin hannunsa na hagu a saman ƙijinsa.
5. Sannan yayi addu'ar buɗe sallah, sai yace: "Ya Allah ka nesantar da tsakanina da kurakuraina kamar yadda ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, ya Allah ka tsaftaceni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farin tufa daga datti, ya Allah ka wankeni daga kurakuraina da ruwa da ƙanƙara da kuma kumfa".
“Subhanakal Lahumma Wabi Hamdika, Tabarakas Muka, Wata’ala Jadduka, Wala’ilaha Gairaka”.
6.Sannan ya nemi tsari, sai yace: "Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa. 7. Sannan yayi Bisimillah, ya karanta Fatiha sai yace: {Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai 1. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai 2. Mai Rahama Mai Jin Qai 3. Mamallakin Rãnar Sakamako 4. Kai kaɗai muke bautawa, kuma Ka kaɗai muke neman taimakonKa. Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya 6. Hanyar waɗanda Kayiwa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi akansuba, kuma ba ɓatattu ba 7}. [Fatiha: 1-7].
Sannan yace: (Amin), yana nufin: Ya Allah ka amsa.
8.Sannan ya karanta abinda ya sawwaƙa na Al-ƙur'ani, sai ya tsawaita karatu a sallar Asuba.
9. Sannan yayi ruku'u: Wato ya sunkuyar da kansa, domin girmamawa ga Allah, ya kuma yi kabbara yayin ruku'insa, sai ya ɗaga hannayensa zuwa daura da kafaɗunsa. Sunnah: Itace ya miƙar da gadon bayansa, ya ɗora kansa daidai dashi, ya ɗora hannayensa akan gwiwowinsa biyu, yana mai wara yatsu.
10. Yana mai cewa acikin ruku'insa: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma}. sau uku, idan kuma ya ƙara da: "Tsarki ya tabbatar maka ya Allah da godiyarka, ya Allah ka gafartamini" to yana da kyau.
11. Sannan ya ɗago kansa daga ruku yana mai cewa: "Allah yaji wanda ya gode masa", sai ya ɗaga hannayensa a wannan lokacin zuwa daura da kafaɗunsa biyu. Mamu kuwa ba zaice: "Allah yaji wanda ya gode masa", kawai a maimakonta sai yace: "Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka".
12. Sannan yace bayan ɗagowarsa: "Ya Ubangijimmu, godiya ta tabbata gareka cikin sammai da ƙasa, da kuma cikin abinda kaso na kowanne abu bayan haka".
13. Sannan yayi sujjadar farko, sai yace ayayin sujjadarsa: "Allahu Akbar", kuma zaiyi sujjadar ne akan gaɓɓai bakwai: Goshi, da hanci, da tafukan hannu biyu, da gwiwowi biyu, da gefunan yatsun ƙafafuwa biyu, sai nisantar da damutsansa daga gefunan jikinsa biyu, kada ya shinfiɗa zangalalin hannayensa biyu akan ƙasa, ya kuma fuskanci Al-ƙibla da kan yatsunsa.
14. Sai yace acikin ruku'insa: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi ɗaukaka" sau uku, idan ya ƙara: "Tsarki ya tabbatar maka ya Allah Ubangijinmu, ya Allah ka gafarta mini" to yana da kyau.
15. Sannan ya ɗago kansa daga sujjada yana mai cewa: "Allah ne mafi girma".
16. Sannan ya zauna tsakanin sujjada biyu, akan diddigensa na hagu, sai ya kafa diddigensa na dama, sai ya ɗora hannunsa na dama akan gefan cinyarsa ta dama, daga inda yake biye da gwiwarsa, sai ya dunƙule ƙaramin yatsa da wanda yake bi masa, sai kuma ya ɗaga manuniya yana mai motsashi a yayin addu'arsa, yana sanya gefan babban yatsa haɗe da yatsan tsakiya kamar kewaye, sai ya ɗora hannunsa na hagu yatsun a shimfiɗe akan gefen cinyarsa ta hagu daga inda yake biye da gwiwa.
17. Sai yace acikin zamasa tsakanin sujjadu biyu: "Ya Ubangijina ka gafarta mini, ka ji ƙaina, ka shiryar dani, ka azurtani, ka datar dani, ka yi mini afuwa".
18. Sannan ya sake yin sujjada ta biyu kamar ta farko cikin abinda ake faɗa, kuma ake aikatawa, ya kuma yi kabbara yayin sujjadarsa.
19. Sannan ya miƙe daga sujjada ta biyun yana mai cewa: "Allah ne mafi girma" yana sallatar raka'a ta biyu kamar ta farko acikin abinda ake faɗa da abinda ake aikatawa, sai dai cewa shi ba zai sake addu'ar buɗe sallah acikinta ba.
20. Sannan ya zauna bayan ƙare raka'a ta biyu yana mai cewa: "Allah ne mafi girma", sai ya zauna kamar yadda ya zauna a tsakanin sujjada biyu daidai wadaida.
21. Sai ya karanta Tahiya a wannan zaman, sai yace: "Gaisuwa ta tabbata ga Allah da addu'oi da kyawawan abubuwa, aminci ya tabbata a gareka, ya kai wannan Annabi, da rahamar Allah da albarkarsa, aminci ya tabbata agaremu da salihan bayin Allah, ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa cewa lallai Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, Allah kayi tsira ga Muhammad da iyalan Muhammad, kamar yadda kayi salati ga Ibrahim da iyalan Ibrahim, lallai kai abin yabone mai girma, kayi albarka ga Muhammad da iyalan Muhammad, kamar yadda kayi albarka ga Ibrahim da iyalan Ibrahim, lallai cewa kai abin yabone kuma mai girma". Sannan sai ya roƙi Ubangijinsa da abinda yaso, na alhairan Duniya da lahira.
22. Sannan yayi sallama a damansa yana mai cewa: "Aminci ya tabbata agareku da rahamar Allah". Da kuma hagunsa kamar haka.
23. Idan sallar ta zama mai raka'a uku ce ko huɗu,ya tsaya inda ƙarshen Tahiyar farko take, shine: "Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lalle Annabi Muhammadu bawansane kuma Manzonsane".
24. Sannan sai ya yunƙura yana mai cewa: "Allah ne mafi girma", yana ɗaga hannayensa zuwa daidai kafaɗunsa a daidai wannan lokacin.
25. Sannan sai ya sallaci abinda yayi saura na sallarsa akan siffar raka'a ta biyu, sai dai cewa shi zai taƙaita ne akan karatun Fatiha kaɗai.
26. Sannan sai ya zauna zama na Tawarruƙ, yana kafa diddigen ƙafarsa tadama, yana kuma fitar da diddigen ƙafarsa ta hagu ta ƙarkashin ƙwaurinsa na dama, sai ya tabbatar da mazauninsa a ƙasa, sai kuma ya ɗora hannuwansa akan cinyoyinsa akan siffar ɗorasu aTahiyar farko.
27. A wannan zaman zai karanta Tahiya ne baki ɗayanta.
28. Sannan yayi sallama a damarsa yana cewa: "Assalamu alaikum warahmatullah". hakama a hagunsa.
Tmbaya ta: 26.Waɗanne zikirai ne za'a yi bayan an sallame daga sallah?
Amsa: "Ina neman gafarar Allah" Sau uku.
"Ya Allah, kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, ka girmama ya ma'abocin girma da ɗaukaka".
-"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai yake bashi da abokin tarayya, mulki nasane, kuma godiya tasace, shine mai iko akan komai. Ya Allah babu mai hanawa ga duk abinda ka bayar, kuma babu mai bayar da abinda ka hana, rabo baya amfanar da mai rabon gareka".
-"Babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai yake bashi da abokin tarayya, mulki nasane kuma godiya tasace, kuma shi mai ikone akan komai, babu dabara, babu ƙarfi sai ga Allah, babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, ba ma bauta wa kowa sai shi, ni'ima tasace, falala tasace, kyakkyawan yabo nasane, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, muna masu tsarkake addini domin shi, ko da kafirai sun ƙi.
-"Tsarki ya tabbata ga Allah" sau talatin da uku.
-"Godiya ta tabbata ga Allah" sau talatin da uku.
-"Allah ne mafi girma" sau talatin da uku.
Sannan cikon ɗarin yace: "Babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai yake, bashi da abokin tarayya, mulki nasane kuma godiya tasace, kuma shi mai iko ne akan komai".
-Sai ya karanta Suratul Ikhalasi, da Falaƙi da Nasi sau uku, bayan sallar Asuba da Magariba, sau ɗaiɗai kuma bayan sauran sallolin.
- Sai ya karanta Ayatul Kursiyyi sau ɗaya.
Tambaya ta 27. Waɗanne ne sunnoni na kullum?, kuma mecece falalarsu?
Amsa: Raka'a biyu kafin Asuba.
Raka'a huɗu kafin Azahar.
Raka'a biyu bayan Azahar.
Raka'a biyu bayan Magariba.
Raka'a biyu bayan Isha.'i.
Falalarsu: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Wanda ya sallaci raka'a goma sha biyu a dare da rana domin neman lada, Allah zai gina masa gida a Aljanna". Muslim da Ahmad ne da wasunsu suka ruwaitoshi.
Tambaya ta: 28.Wacce rana ce mafi falala a mako?
Amsa: Ranar Juma'a, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Lalle yana daga cikin mafificin ranakunku ranar Juma'a, acikintane aka halicci Annabi Adam, kuma acikintane aka karɓi rayuwarsa, kuma acikintane za'a busa ƙaho, kuma acikintane za'a mutu, ku yawaita yin salati agareni acikinta, domin salatinku abin bijirowane agareni". Yace: Sukace Ya Ma'aikin Allah, to yaya za a bijiro da salatimmu agareka alhali haƙiƙa ka dandaƙe? - suna cewa ka dandaƙe - sai yace: "Lalle Allah - mai girma da ɗaukaka - ya haramta wa ƙasa jikin Annbawa". Abu Daud da waninsane suka ruwaitoshi.
Tambaya ta: 29. Menene hukuncin sallar Juma'a?
Amsa: Farilace akan kowanne musulmi namiji baligi mai hankali mazauni.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai kutaho zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri agareku idan kun kasance kunã sani}. [Surat Al-Munafiƙun: 9].
Tambaya ta 30: Nawa ne adadin raka'o'in sallar Juma'a?
Amsa: Adadin rakao'in sallar Juma'a raka'o'i biyu ne, liman yana bayyanar da karatunsu, huɗubobi biyu sanannu suna gabatarsu.
Tambaya: 31. Shin ya halatta ƙin zuwa sallar Juma'a?
Amsa: Ba ya halatta ƙin zuwa sallar Juma'a, saidai idan akwai wani halataccen uzuri, yazo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - faɗinsa: "Wanda ya bar Juma'a uku dan wulaƙantarwa, Allah zaiyi rufi akan zuciyarsa". Abu Daud ne da waninsa suka ruwaitoshi.
Tambaya ta 32: Ka ambaci sunnoin ranar Juma'a.
Amsa:
1. Wanka.
2. Shafa turare.
3. Sanya mafi kyan tufafi.
4. Zuwa masallaci da wuri.
5.Yawaita salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
6. Karatun Suratul Kahf.
7. Tafiya zuwa masallaci da ƙafa.
8. Kardadon lokacin amsa addu'a.
Tambaya ta: 33. Ka ambaci falalar sallar Jam'i.
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah ya yarda dasu - lallai cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Sallar Jam'i tafi sallar mutum ɗaya da daraja ashirin da bakwai. Muslim ne ya ruwaitoshi.
Tambaya ta: 34. Menene khushu'i acikin sallah?
Amsa: Shine halartar da zuciya da nutsuwar gaɓɓai.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Hakika mũminai sun rabauta}. {Waɗanda su suke yin khushu'i acikin sallarsu}. [Surat Al-Muminun: 1,2].
Tambaya ta: 35 Mecece Zakkah?
Amsa- Ita haƙƙi ce na wajibi a dukiya keɓantacciya ga wata jama'a keɓantacciyya a lokaci keɓantacce.
- Kuma ita rukuni ce daga cikin rukunan Musulunci, kuma sadaka ce ta wajibi da ake karɓa daga mawadaci a bada ita ga mabuƙaci.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Kuma suka bada Zakkah}. [Surat Al-Baƙarah: 43].
Tambaya ta:36. Mecece sadaka ta mustahabbi (Wacce ake so)?
Amsa- Itace wacce ba zakkah ba, kamar: Yin sadaka ta fuskokin alheri kuma akowane lokaci.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Ku ciyar acikin tafarkin Allah}. [Surat Al-Baƙarah: 195].
Tambaya ta 37. Kayi bayanin Azimi?
Amsa- Shine yin bauta sabo da Allh ta hanyar kamewa daga barin abinda ke karya azumi, tun daga hudowar Alfiji har zuwa faɗuwar rana tare da niyya, shi kashi biyune:
Azumin wajibi: Kamar Azumin watan Ramadan, shi kuma rukuni ne daga cikin rukunan musulunci.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa}. [Surat Al-Baƙarah: 183].
Da Azumin da bana wajibi ba: Kamar Azumin ranar Litinin da Alhamis a kwanne sati, da Azumin kwanaki uku a kowanne wata, mafificin su kuma sune fararan kwanaki (13,14,15) na kowanne watan Musulunci.
Tambaya ta 38. Ka ambaci falalar Azumin watan Ramadan?
Amsa- Daga Abu Huraira - Allah ya yarda dashi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa". An haɗu akansa (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Tambaya ta 39. Ka ambaci falalar Azumin nafila?
Amsa- Daga Abu Sa'id Al-Khudri- Allah ya yarda dashi - yace: Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Babu wani bawa da zaiyi Azumin wani yini ɗaya domin Allah, face sai Allah ya nesantar da fuskarsa daga wuta sanadiyyar wannan Azumin shekara saba'in". An haɗu akansa (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
- Ma'ana "Kharif saba'in" wato; Shekara saba'in.
Tambaya ta 40. Ka ambaci wasu daga cikin masu ɓata Azumi?
Amsa- 1- Ci da sha da gangan.
2. Kakalo amai da gangan.
3. Ridda daga musulunci.
Tambaya ta 41. Menene Sunnonin Azumi?
Amsa-1- Gaggauta buɗa baki.
2. Sahur da kuma jinkirtashi.
3. Kari akan ayyukan alheri da kuma ibada.
4. Faɗar mai Azumi idan aka zageshi: Lallai ni ina Azumi.
5. Yin addu'a a lokcin buɗa baki.
6. Yin buɗa baki da ɗanyen dabino ko busasshe, idan kuma bai samu ba sai yayi da ruwa.
Tambaya ta 42: Ka faɗi ma'anar Hajji?
Amsa: Hajji: Shine yin bauta ga Allah - maɗaukain sarki - da nufin ɗakinsa mai alfarma domin gabatar da wasu ayyuka keɓantattu, a lokaci keɓantacce.
Allah Maɗaukakin sarki yace: {Kuma akwai Hajjatar ɗaki domin Allah akan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa gareshi wanda ya kafurce to lallai Allah mawadacine ga barin talikai}. [Surat Aal Imran: 97].
Tambaya ta: 43. Ka lissafa rukunan Hajji?
Amsa: 1. Harama (Niyya).
2. Tsayuwar Arafah.
3.Dawafin Ifadah.
4. Tafiya tsakanin Safa da Marwa.
Tambaya ta: 44. Menene falalar aikin Hajji?
Amsa- Daga Abu Huraira - Allah ya yarda dashi - yace: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yana cewa: "Wanda yayi Hajji, bai yi kwarkwasa ba, kuma bai yi fasikanci ba, zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifeshi". Bukhari da waninsa ne suka rawaito shi.
- "Kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifeshi" Wato ba tare da wani zunubi ba.
Tambaya ta: 45. Kafaɗi ma'anar Umrah?
Amsa: Umara ita ce bauta wa Allah da niyyar fuskantar ɗakinsa mai alfarma domin gabatar da ayyuka keɓantattu, a lokaci keɓantacce.
Tambaya ta 46. Ka lissafa rukunan Umarah?
Amsa: 1. Harama (Niyya).
2. Dawafin a ɗakin Ka'abah.
3. Tafiya tsakanin Safa da Marwa.
Tambaya ta 47. Menene jihadi domin ɗaukaka addinin Allah?
Amsa: Shine bada ƙoƙari domin yaɗa Addinin musulunci da kuma kare shi, da ma abotansa, ko kuma yaƙar maƙiyi ga musulunci da ma abotansa.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Kuyi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani}. [Surat Al-Tubah: 41].
BANGARAN TARIHIN ANNABI (TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA AGARESHI).32
Tambaya ta 1. Mecece Nasabar Annabin mu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -?
Amsa: Shi ne Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdulmuɗallabi ɗan Hashim. Shi Hashim daga Kuraishawa yake, su kuma Kuraishawa daga Larabawa suke, su kuma Larabawa daga zuriyar Annabi Isma'il suke, Isma'il kuma ɗan Annabi Ibrahim - tsira da amincin Allah su agareshi - da kuma Annabin mu.
Tambaya ta 2. Menene sunan mahaifiyar Annabin mu - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -?
Amsa: Sunanta Amina 'yar Wahab.
Tambaya ta 3. Yaushe ne babansa ya rasu?
Amsa; Babansa ya rasu ne a Madina alhali shi yana ciki, ba'a ma haifeshi ba - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Tambaya ta: 4. Yaushe akan haifi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -?
Amsa: A shekarar giwa, ranar Litinin daga watan Rabi'ul Awwal.
Tambaya ta 5. A wanne gari aka haifeshi?
Amsa: A cikin Makkah.
Tambaya ta: 6. Su waye suka shayar dashi kuma suka reneshi bayan mahaifiyarsa?
Amsa: Baiwar babansa Ummu Aiman.
- Baiwar babbanfansa Abu Lahab, Suwaiba.
- Haimat Al-Sa'adiyya.
Tambaya ta 7. Yaushe babar shi ta rasu?
Amsa: Babar shi ta rasune alhali shi yana ɗan shekara shida, sai kakan sa Abdulmuɗallabi ya reneshi.
Tambaya ta 8. Waye yareneshi bayan mutuwar kakansa Abdulmuɗallabi?
Amsa: Kakansa Abdulmuɗallabi ya rasu alhali shi yana da shekara takwas, sai baffansa Abu Dalib ya reneshi.
Tambaya ta : 9 Yaushe ne yayi tafiya tare da baffansa zuwa Sham?
Amsa: Yayi tafiya tare da baffansa zuwa Sham alhali shekarunsa shekara goma sha biyu ne.
Tambaya ta: 10. Yaushe ne tafiyar sa ta biyu ta kasance?
Amsa: Tafiyar sa ta biyu ta kasance ne ta fatauci da dukiyar Nana Khadija - Allah ya yarda da ita -, yayin da ya dawo sai ya aureta - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -, alhali yana da shekaru ashirin da biyar.
Tambaya: 11. A yaushe ne Kuraishawa suka sake gina Ka'aba?
Amsa: Kuraishawa sun sake gina Ka'aba ne a lokacin yana da shekara talatin da biyar.
Sai suka sa shi mai yanke hukunci a tsakanin su yayin da suka yi saɓani akan wa zai sanya baƙin dutse, sai ya sanya shi a wani tufafi, ya kuma umarci kowacce ƙabila ta kama gefen tufafin, sun kasance ƙabilu huɗu, da suka ɗaga shi zuwa bigirensa, sai - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya sanya shi da hannunsa.
Tambaya ta 12. Nawa shekarunsa suka kasance alokacin da aka aikoshi? Kuma zuwa ga wa aka aikoshi?
Amsa: Shekarunsa sun kasance Arba'in ne kuma an aikoshi ne zuwa ga mutane baki ɗaya mai bushara kuma mai gargaɗi.
Tambaya ta 13. Menene farkon abinda aka farayi masa wahayi dashi?
Amsa: Mafarki na gaskiya, ya kasance ba ya ganin mafarki face ya zo kamar ɓullowar Asuba.
Tambaya ta: 14. Ya halayyarsa take kafin a fara yi masa wahayi? kuma yaushe ne wahayi ya sauka gareshi a karon farko?
Amsa: Ya kasance yana bauta wa Allah a kogan Hira, kuma yana yin guzuri saboda hakan.
Kuma wahayi ya sauka a gare shi, alhali yana kogon Hira yana bauta wa Allah.
Tambaya ta 15.Mene ne farkon abinda yasauka a gare shi na Al-ƙur'ani?
Amsa: Faɗin Allah -maɗaukakin sarki -: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda yayi halitta 1. Ya halicci mutum daga gudan jini 2. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shine mafi girma 3. Wanda Ya sanar (da mutum) da alƙalami 4. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba}. [Surat Al-alaq: 1-5].
Tambaya ta 16. Waye farkon wanda yayi imani da manzancinsa?
Amsa: Daga cikin maza: Abubakar Siddiƙ, daga cikin mata: Nana Khadija 'yar Khuwailid, daga cikin yara: Aliyu ɗan Abu Dalib, daga cikin 'yantattu: Zaidu ɗan Harisah,daga cikin bayi: Bilal ɗan Rabah, da Allah ya yarda da su da wasunsu.
Tambaya ta: 17. Yaya Da'awa zuwa Musulunci ta kasance?
Amsa: Da'awar ta kasance ne a ɓoye wajen shekaru uku, sannan sai Ma'aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yayi umarnin bayyanar da Da'awar.
Tambaya ta: 18. Ya halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya kasance da waɗanda suka yi imani dashi bayan bayyanar da Da'awah?
Amsa: Mushirikai sun kai matuƙa wurin cutar dashi da cutar da musulmai, har sai da yayi izini ga muminai da Hijira zuwa wurin Najashi a Habasha.
Ma abota shirka suka haɗu akan cutarwa da kuma kashe Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -, sai Allah ya tsare shi, ya kewaye shi da baffansa Abu Dalib domin ya tsare shi daga garesu.
Tambaya ta: 19. Waye ya rasu a shekara ta goma daga aikoshi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -?
Amsa: Baffansa Abu Dalib ya rasu, da kuma mai ɗakinsa Nana Khadija - Allah ya yarda da ita -.
Tambaya 20. A yaushe ne aka yi Isra'i da Mi'iraji?
Amsa: Hakan ya kasance ne a shekaru hamsin daga rayuwarsa, kuma aka wajabta masa salloli biyar.
Isra'i: Shi ne tafiya daga Masallaci mai alfarma zuwa Masallaci mafi nisa (Kudus).
Mi'iraji: Ya kasance ne daga Masallaci mafi nisa (Kudus) zuwa sama har zuwa magaryar tuƙewa.
Tambaya ta: 21. Ya Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya karance yakewa mutane Da'awa a wajan Makkah.
Amsa: Ya kasance yana kiran mutanan Da'ifa, kuma yana zuwa wuraran taruka da matattarar mutane, har mutanan Madina daga cikin Ansar sukazo, suka yi imani da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - kuma suka yi masa caffa akan taimaka masa.
Tambaya ta: 22. Kwana nawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya wanzu a Makka yana kiran mutane?
Amsa: Ya wanzu ne tsawon shekara goma sha uku.
Tambaya ta: 23. Zuwa ina Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yayi Hijira?
Amsa: Daga Makkah zuwa Madina.
Tambaya ta:24. Shekara nawa ya wanzu a Madina?
Amsa: Shekaru goma.
Tambaya ta:25.Me aka wajabta masa a Madina na Shari'o'in musulunci?
Amsa: An wajabta masa Zakka, da Azumi da Hajji, da Jihadi, da kiran sallah, da wasunsu na Shari'o'in musulunci.
Tambaya ta 26. Waɗanne ne manyan yaƙoƙin sa?
Amsa: Babban yaƙin Badar.
Yaƙin Uhud.
Yaƙin Taron dangi.
Yakin Buɗe Makka.
Tambaya ta 27.Mene ne ƙarshen abinda yasauka na Al-ƙur'ani?
Amsa: Faɗinsa - maɗaukakin sarki -: {Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su 281}. [Surat Al-Baƙarah: 281].
Tambaya ta: 28. Yaushe Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya rasu ? kuma shekaru nawa?
Amsa: Ya rasu a watan Rabi'ul Awwal, a shekara ta goma sha ɗaya daga Hijira, yana da shekaru sittin da uku.
Tambaya ta 29. Ka ambaci matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Amsa: 1. Nana Khadija 'yar Khuwailid -Allah ya yarda da ita -.
2. Nana Saudatu 'yar Zam'ah - Allah ya yarda da ita -.
3. Nana A'isha 'yar Abubakr - Allah ya yarda da ita-.
4. Nana Hafsatu 'yar Umar - Allah ya yarda da ita -.
5. Nana Zainab 'yar Khuzaimah - Allah ya yarda da ita -.
6. Ummu Salamah Hindu 'yar Abu Umayya - Allah ya yarda da ita -.
7. Ummu Habiba Ramlatu 'yar Abu Sufyan - Allah ya yarda da ita -.
8. Juwairiyya 'yar Haris - Allah ya yarda da ita -.
9. Maimuna 'yar Haris - Allah ya yarda da ita -.
1.Safiyya 'yar Hayayi - Allah ya yarda da ita -.
11. Zainab 'yar Jahash - Allah ya yarda da ita -.
Tambaya ta: 30. Su waye 'ya'yansa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi?
Amsa: Daga cikin maza akwai uku:
1.Alƙasim, da shi yakasance ake masa alkunya.
Da Abdullahi.
Da Ibrahim.
Daga mata kuma akwai:
Fatima.
Ruƙayyah.
Ummu Kulsum.
Zainab.
Dukkanin 'ya'yansa daga Nana Khadija ne - Allah ya yarda da ita - in banda Ibrahim, kuma dukkanin su sun rasu kafin sa in banda Fatima, ta rasu bayan sa da watanni shida.
Tambaya ta: 31. Ka ambaci wasu daga siffofin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat a gare shi - na halitta.
Amsa: Ma'aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance tsaka tsaki ne cikin mutane, ba gajere bane kuma ba dogo bane, kai ya kasance tsakanin haka, ya kasance fari ne da sirkin ja - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance mai kaurin gemu ne, mai yalwatattun idanuwa, mai yalwataccan baki, gashinsa mai tsananin baƙi ne, mai faɗin kafaɗu ne, mai daɗin ƙanshi ne, da wanin haka na kyakykyawar halittarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Tambaya ta 31. Akan me Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bar al'ummar sa?
Amsa: Ya bar al'ummar sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - akan hanya fara ƙal, daranta kamar hantsinta, babu wanda yake karkata daga gareta sai halakakke, babu wani alheri da ya bari face sai da ya shiryar da al'umma a kansa, haka kuma babu wani sharri sai da ya tsoratar da ita daga gareshi.
BANGARAN TAFSIRI17
Tambaya ta 1.Karanta Fatiha ka fassarata?
Amsa: Suratul Fatiha da kuma Tafsirinta.
{Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai 1. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai 2. Mai Rahama Mai Jin ƙai 3. Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako 4. Kai kaɗai muke bautawa, kuma Ka kaɗai muke neman taimakonKa 5. Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya 6. Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi akan su ba, kuma ba ɓatattu ba 7}. [Fatiha: 1-7].
FASSARA:
An ambaceta Suratul Fatiha ne؛ domin buɗe littafin Allah da ita.
🎧 1- {Da sunan Allah mai yawan rahama ma yawan jinƙai 1.} Ma'ana: Da sunan Allah nake fara karatun Al-ƙur'ani, ina mai neman taimako da shi - maɗaukakin sarki - ina mai neman albarka da ambaton sunan sa.
{Allah}. Wato: Abin bautawa da gaskiya, kuma ba'a ambaton wanin sa da shi - tsarki ya tabbatar masa.
{Ar-Rahman}. Wato: Ma'abocin yalwatacciyar rahama, wacce rahamar sa ta yalwaci dukkan komai.
Arrahim.Mai keɓantacciyar rahama ga muminai kaɗai.
🎧 2- {Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}. Wato: Dukkanin nau'ukan yabo da cika sun tabbata ga Allah shi kaɗai.
🎧 3. {Mai yawan rahama mai yawan jin ƙai}. Wato: Mai yalwatacciyar rahama, wacce ta yalwaci kowanne abu, kuma ma'abocin rahama mai saduwa ga muminai.
🎧 4. {Mamallakin ranar sakamako}. Itace ranar Al-ƙiyama.
🎧 5. {Kai kaɗai muke bautawa kuma gareka kaɗai muke neman taimako}. Wato: Muna bauta maka kai kaɗai kuma muna neman taimako da kai kai kaɗai.
🎧 6. {Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya}. Itace shiriya zuwa Musulunci da kuma Sunnah.
🎧 7. {Hanyar waɗanda ka yi ni'ima agaresu , ba waɗanda ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba 7}. Wato: Tafarkin bayin Allah na gari daga Annabawa da waɗanda suka biyo su, ba hanyar Nasara da Yahudu ba.
-An sunnanta bayan karanta ta yace (AMIN) wato: Ka amsa mana.
Tambaya ta: 2. Ka karanta Suratul Zalzala. kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratul Zalzala da kuma Tafsirinta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
{Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta 1. Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi 2. Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta 3?. A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta 4. Da cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta 5. A rãnar nan mutane zasu fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu 6. To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi 7. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi 8. [Surat Al-Zilzilah; 1 - 8].
FASSARA:
🎧 1- {Idan aka girgiza ƙasa girgizawar nan tata}. Idan aka motsa ƙasa motsawa mai tsanani wanda zai faru gare ta a ranar Al-ƙiyama.
🎧 2- {Kuma ƙasa ta fitar da naunye nauyen nan na ta 2}: Kasa ta fitar da duk abinda yake cikinta na matattu da waninsu.
🎧 3. {Kuma mutum ya ce me ya sa me ta 3}. Mutum yana mai ɗimaucewa sai ya ce: Wanne al'amari ƙasa take ciki tana motsawa kuma tana bugawa?
🎧 4. A wannan ranar za ta ba da labarinta 4}: Acikin wannan yinin mai girman ƙasa za ta bada labari da abinda aka aikata akanta na alkhairi ko na sharri.
🎧 5. {Saboda Ubangikinka ya yi mata wahayi 5}: Domin cewa Allah Ya sanar da ita kuma Ya umarce ta da hakan.
🎧 6. {Awannan ranar mutane za su fito daban daban domin a nuna musu ayyukansu 6}. A wannan yini mai girman ne wanda ƙasa take girgiza acikinsa, mutane za su fito daga matsayar hisabi a rarrabe؛ domin su ga ayyukan su da suka aikata su a nan duniya.
🎧 7. {Wanda ya aikata nauyin komayya na alheri zai gan shi 7}: Wanda ya aikata nauyin ƙaramar tururuwa na ayyukan alheri da biyayya zai gan shi a gabansa.
🎧 8. {Wanda ya aikata nauyin komayyana na sharri zai gan shi 8}: Haka kuma duk wanda ya aikata nauyinta na ayyukan sharri zai gan shi a gaban sa.
Tambaya ta: 3. Ka karanta Suratul Adiyat, kuma ka fassarata.
Amsa: Suratul Adiyat da kuma fassararta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ina rantsuwa da dawakai masu gudu suna fitar da kukan ciki 1. 2. Masu ƙyasta wuta ƙyastawa 2. 3. Sannan masu kai hari a loakcin Asuba 3. 4.Sai su motsar da ƙũra game da shi 4. 5. Sai su shiga, game da ita (ƙurar) a tsaknin jama'ar maƙiya 5. 6. Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijin sa 6. 7. Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifin sa akan haka 7. 8. Kuma lallai ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne 8. 9. Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin ƙaburbura 9. 10.Aka bayyana abin da ke cikin zukata 10. 11. Lalle ne Ubangijin su, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne? [Surat Al-Adiyat: 1 - 11].
FASSARA:
🎧 1. {Ina rantsuwa da dawakai masu gudu suna fitar da kukan ciki 1}: Allah Ya rantse da dawakai masu gudu har ake jin kukan cikin su saboda matsanancin gudu.
🎧 2. {Masu ƙyasta wuta ƙyastawa}: Kuma Allah ya rantse da dawakai waɗanda suke ƙyastawa da kofatansu idan suka taka duwatsu, saboda tsananin takawar akan su.
🎧 3. {Masu kai hari da Asuba 3}: Kuma Allah ya rantse da dawakai waɗanda suke kai hari ga abokan gaba a lokacin Asuba.
🎧 4. {Sai su motsar da ƙura game da shi 4}: Sai su motsar da ƙura saboda gudun su.
🎧 5. {Sai su shiga, game da ita a tsakanin jama'a maƙiya 5}: Sai su shiga tsakiya da sadaukan su gaba ɗaya daga maƙiya.
🎧 6. {Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa 6}: Lallai mutum mai hanawane ga alherin da Ubangijin sa Ya ke nufin sa daga gare su.
🎧 7. {Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifin sa da haka 7}: Lallai cewa shi mai shaida ne akan hanawar sa ga alheri. kuma ba zai taɓa musun haka ba saboda bayyanar sa.
🎧 8.{Kuma lalle ne shi ga dukiya shi mai tsananin so ne 8}: Lallai cewa shi saboda tsananin son sa ga dukiya yana rowa da ita ne.
🎧 9. {Shin, ba ya sanin cewa idan aka tone abin da yake cikin ƙaburbura 9}: Shin yanzu wannan mutumin mai ruɗuwa da rayuwar duniya idan Allah Ya tayar da waɗanda ke cikin ƙabarbura na matattu, kuma ya fito da su zuwa doran ƙasa domin hisabi da sakamako, to lalle al'amarin bai kasance kamar yanda yake tsammani ba?!
🎧 10. {Aka bayyana abinda ke cikin zukata 10}: Kuma aka futo, aka bayyanar da abinda yake cikin zukata na niyyoyi, da ƙudurce-ƙudirce da wasun su.
🎧 11. {Lalle ne Ubanginsu game da su a ranar nan, mai ƙididdiga ne 11}: Wato lalle Ubangijinsu dangane da su a wannan ranar wanda zai ba su labari ne, babu wani abinda yake ɓoyuwa a gare shi na al'amarin bayin sa, kuma zai yi musu sakayya akan hakan.
Tambaya ta: 4. Ka ranta Suratul Qari'ah? kuma ka fassarata.
Amsa: Suratul Qari'ah da kuma fassararta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Mai ƙwanƙwasa 1. 2.Mece ce mai ƙwanƙwasar 2? 3. Kuma wane ne ya sanar da kai abin da ake nufi da Maƙwanƙwashiya 3? 4. Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa 4. 5.Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe 5. 6. To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi 6. 7. Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda 7. 8. Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi) 8. 9. To uwarsa Hawiya ce 9. 10 Kuma me ya sanar da kai mece ce ita 10? 11. Wata wuta ce mai zafi 11}. [Surat Al-Qari'ah: 1 - 11].
FASSARA:
🎧 1- {Mai ƙwanƙwasa 1}. Al-ƙiyama tana ƙwanƙwasa akan zukatan mutane saboda girman tashin hankalinta.
🎧 2. {Mece ce mai ƙwanƙwasa 2}: Mece ce wannan Al-ƙiyamar wacce take ƙwanƙwasar zukatan mutane saboda girman tashin hankalinta?!.
🎧 3. {Kuma me ya sanar da kai mecece mai ƙwanƙwasa 3}: Mene ne ya sanar da kai - ya kai wannan Manzo - mecece wannan Al-ƙiyamar wacce take ƙwanƙwasar zukatan mutane, saboda girman sha'aninta, lalle itace ranar Al-ƙiyama.
🎧 4. {Ranar da mutane zasu kasance kamar 'ya'yana fari masu watsuwa 4}: Ranar da zata ƙwanƙwashi zukatan mutane su kasance kamar fari masu yaɗuwa masu tarwatsewa nan da can.
🎧 5. {Kuma duwatsu su kasance kamar gashin sufin da aka saɓe}: Duwatsu su kasance kamar gashin sufi wanda aka saɓe, acikin sakin tafiyar su da motsin su.
🎧 6. {To, amma wanda ma'aunan sa suka yi nauyi 6}: Amma wanda kyawawan ayyukan sa suka rinjayi munanan ayyukan sa.
🎧 7. {To, shi yana cikin wata rayuwa yardadda 7}: Shi yana cikin rayuwa yardadda da zai sameta a cikin Aljanna.
🎧 8. {To, amma duk wanda ma'aunansa suka yi sauƙi 8}: Amma wanda munanan ayyukansa suka rinjayi kyawawan ayyukansa.
🎧 9. {To, Uwar sa Hawiyace 9}: Masaukin sa da madabbatar sa a ranar Al-ƙiyama ita ce Jahannama.
🎧 10. {Kuma me ya sanar da kai menene ita 10}: Me ya sanar da kai - ya kai wannan Manzo - mecece ita?!
🎧 11. {Wata wuta ce mai zafi}: Ita wuta ce mai tsananin zafi.
Tambaya ta: 5. Ka ranta Suratul Takasur, kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratut Takatur da fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Alfahari da yawan dukiya da dangi ya shagaltar da ku 1. .2. Har kuka ziyarci maƙabartu 2. 3. A'aha! (Nan gaba) zã ku sani 3. 4.A'aha! dai (Nan gaba) zã ku sani 4. 5. Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni 5. 6.Lalle ne zakuga Jahim 6. 7. Sannan kuma lalle ne za ku ganta da idanu, bayyane 7. 8. Sannan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku) 8. [Surat At-Takasur: 1 - 8].
FASSARA:
🎧 1. {Alfahari da yawan dukiya da dangi ya shagaltar da ku 1}: Alfahari da dukiya da kuma 'ya'ya sun shagaltar da ku - yaku mutane - daga bin Allah.
🎧 .2. {Har kuka ziyarci maƙabartu 2}: Har kuka mutu kuka shiga ƙaburburan ku.
🎧 3. {A'aha! (Nan gaba) zã ku sani 3}: Abinda yakasance tare da ku har alfahari ya shagaltar da ku daga ƙin bin Allah, to da sannu za ku san ƙarshen wannan shagaltarwar.
🎧 4. {A'aha! dai (Nan gaba) zã ku sani 4}: Sannan za ku san ƙarshensa.
🎧 5. {Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni}:Tabbas da a ce ku kuna sani na haƙiƙanin cewa lalle ku za'a tasheku a gaban Allah, kuma zai saka muku akan ayyukan ku, da ba ku shagaltu da alfahari da dukiya da kuma 'ya'yaba.
🎧 6. {Lalle ne zaku ga Jahim 6}: Kuma wallahi sai kunga wuta a ranar Al-ƙiyama.
🎧 7. {Sannan kuma lalle ne za ku ganta da idanu, bayyane 7}:Sannan tabbas zaku ganta gani na haƙiƙa da babu kokwanto acikin sa.
🎧 8. (Sannan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku) 8}: Sannan kuma tabbas sai Allah ya tambaye ku a kan hakan a ranar akan abin da yayi muku na ni'ima kamar lafiya da wadata da wasunsu.
Tambaya ta: 6. Ka ranta Suratul Asr, kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratul Asr da kuma fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ina rantsuwa da zamani 1. 2. Lalle ne mutum yana a cikin hasara 2. 3.Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma sukai wasiyya da gaskiya kuma sukai wasiyya da yin haƙuri 3. [Suratul Asr: 1 - 3].
FASSARA:
🎧 1. {Ina rantsuwa da zamani 1} Allah - tsarki ya tabbatar masa - ya yi rantsuwa da zamani.
🎧 2. (Lalle ne mutum yana a cikin hasara 2}: Wato: Dukkanin mutum yana cikin tawaya da kuma halaka.
🎧 3. {Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma sukai wasiyya da gaskiya kuma sukai wasiyya da yin haƙuri 3}: Sai dai wanda ya yi imani kuma ya yi aiki na ƙwarai, tare da haka suka yi kira zuwa ga gaskiya, kuma suka yi haƙuri akansa, to waɗannan sune waɗanda suka tsira daga hasara.
Tambaya ta: 7. Ka ranta Suratul Humaza, kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratul Humaza da kuma fassararta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa) 1. 2. Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa 2. 3. Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi 3. 4. A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama 4. 5. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Huɗama 5? 6. Wutar Allah ce wadda ake hurawa 6. 7. Wadda take lẽƙãwa a kan zukata 7. 8. Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu 8. 9. A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu 9}. [Surat Al-Humazah: 1 - 9].
FASSARA:
🎧 1. Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa) 1}: Azaba da tsananin azaba ta tabbata ga dukkan wanda yake yin gulmar mutane da suka acikin su.
🎧 2. {Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa 2}: Wanda shi himmar sa ita ce tara dukiya da lissafa ta, ba shi da wata himma in ba haka ba.
🎧 2. {Yana zatan cewa dukiyarsa zata dawwamar dashi 3}: Yana zatan cewa dukiyar sa wacce ya tarata zata tseratar da shi daga mutuwa, zai wanzu yana madawwami acikin rayuwar duniya.
🎧 4. (A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama 4}: Al'amarin ba kamar yadda wannan jahilin yake hasashe ba ne, tabbas sai an watsa shi a wutar Jahannama wacce take niƙe ta karya duk abinda aka watsa a cikinta saboda tsananin masifar ta.
🎧 5. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Huɗama?Me ya sanar da kai - Ya kai wannan Manzo mai girma- mece ce wannan wutar wacce take haɗe duk abin da aka watsa cikinta?!
🎧 6. {Wutar Allah ce wadda ake hurawa 6}: Lallai cewa ita wutar Allah ce abar rurawa.
🎧 7. {Wadda take lẽƙãwa a kan zukata 7}: Wacce take zarcewa daga cikin jikkunan mutane zuwa zuciyoyin su.
🎧 8. {Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu 8}: Ita abar kullewace akan waɗanda ake azabtarwa acikin ta.
🎧 9. {A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu 9}: Da wasu turaku miƙaƙƙu dogaye ta yadda bazasu iya fita daga gare ta ba.
Tambaya ta: 8. Ka ranta Suratul Fil, kuma ka fassara ta.
Amsa- Suratul Fil da kuma fassararta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba 1? 2. Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba 2? 3. Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a 3. 4. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta 4. 5. Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye 5. [Surat Al-Fil: 1 - 5].
FASSARA:
🎧 1. {Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba 1?} Ashe ba ka sani ba - ya kai wannan Manzo - yadda Ubangijin ka Ya yi da Abraha ba, shi da mutanan sa ma'abota giwaye,yayin da suka yi nufin rushe Ka'aba?
🎧 2. {Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba 2?} Haƙiƙa Allah ya mayar da mummunan makircinsu na ruishe Ka'abah acikin tozarta, basu sami abinda sukayi buri na kawar da mutane daga Ka'aba, kuma ba su sami komai daga gare ta ba.
🎧 3. {Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a 3}: Kuma ya aika musu da tsuntsaye suka je musu jama'a jama'a.
🎧 4. {Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta 4}: Suna jifansu da duwatsu na taɓo masu tsananin zafi.
🎧 5. {Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye 5}: Sai Allah Ya mayar da su kamar ganyan karmami da dabbobi suka cinye shi kuma suka take shi.
Tambaya ta: 9. Ka ranta Suratl Kuraish? kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratu Kuraishi da fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Saboda sabon Kuraishawa 1. 2. Sabonsu na tafiyar hunturu da ta bazara 2. 3. Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka'abah) 3. 4. Wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro 4. [Surat Kuraish: 1 - 4].
FASSARA:
🎧 1. {Sabon da Kuraishawa sukayi 1}: Abin nufi da wannan shine abinda suka kasance suna sabo da shi daga tafiya acikin hunturu da bazara.
🎧 2. {Sabonsu na tafiyar hunturu da ta bazara 2}: Tafiyar hunturu zuwa Yaman, da tafiyar bazara zuwa ƙasar Sham suna amintattu.
🎧 3. {Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka'abah) 3}: Sai su bautawa Ubangijin wannan ɗakin mai alfarma shi kaɗai, wanda ya sawwaƙe musu wannan tafiya, kada su haɗa shi da kowa wurin bauta.
🎧 4. {Wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro 4}: Shi ne wanda Ya ciyar da su daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga tsoro, na abin da Ya sanya azukatan Larabawa na girmama wannan Harami, da girmama mazauna wurin.
Tabaya ta 10: Karanta Suratul Ma'un, kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratul Ma'un da kuma fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako 1? 2. To, wannan shi ne ke tunkuɗe marãya (daga haƙƙinsa) 2. 3. "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci 3. 4. To, bone ya tabbata ga masu yin salla 4. 5. Waɗanda sune masu shagala daga sallar su 5. 6. Waɗanda sune suke yin riya (ga ayyukan su) 6. 7. Kuma suna hana taimako 7}. [Surat Al-Ma'un: 1 - 7].
FASSARA:
🎧 1. {Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako 1?}: Shin kasan wanda yake ƙaryata sakamako a ranar Al-ƙiyama?!
🎧 2. {To, wannan shi ne ke tunkuɗe marãya (daga haƙƙinsa) 2.To shi ne wannan wanda ya ke tunkuɗe maraya da ƙarfin gaske daga barin buƙatun sa.
🎧 3. {Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci 3}: Ba ya kwaɗaitar da kansa ba kuma ya kwaɗaitar da waninsa akan ciyar da mabuƙaci.
🎧 4. {To, bone ya tabbata ga masu yin sallah 4}: Hallaka da azaba sun tabbata aga masu sallah.
🎧 5. {Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu 5}: Waɗanda sune dangane da sallar su suna wasa da ita ba sa damuwa da ita har lokacinta ya fita.
🎧 6. {Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu) 6}: Wato su ne waɗanda suke nuna sallar su da ayyukansu, ba sa yin aiki domin Allah.
🎧 7. {Kuma suna hana taimako 7}: Suna hana taimakon wasu a abin da babu wata cutarwa a taimakon da shi.
Tambaya ta: 11. Ka karanta Suratul Kausar, kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratul Kausar da kuma fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
{Lalle ne Mu, Mun baka alheri mai yawa 1. 2. Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke (baiko, wato sukar raƙumi) 2. 3. Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka 3}. [Surat Al-kausar: 1 - 3].
FASSARA:
🎧 1. {Lallai ne mu munbaka alheri mai yawa 1}: Lallai mu munzo maka - ya kai wannan Manzo - da alheri mai yawa, daga cikinsa akwai ƙoramar Al-kausara acikin Aljanna.
🎧 2. {Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke (baiko, wato sukar raƙumi) 2}: Sai ka bada godiyar Allah akan wannan ni'ima, ta hanyar yin sallah saboda shi kaɗai, kuma ka yi yanka, saɓanin abin da mushurukai suke aikata shi na neman kusanci ga gumakan su da yankan.
🎧 3. {Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka 3}: Lalle mai ƙinka to shi ne abin yankewa daga dukkanin alheri, abin mantawa wanda in za'a ambace shi za'a ambace shi ne da mummuna.
Tambaya ta: 12. Ka karanta Suratul Kafirun? kuma ka fassarata.
Amsa: Suratul Kafirun da fassararta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ka ce: "Ya kũ kãfirai 1. "Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba 2 Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba 3. Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba 4. {Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba 5. Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni 6}. [Surat Al-Kafirun: 1 - 6].
FASSARA:
🎧 1. Ka ce: {Ya kũ kãfirai 1} Ka ce -Ya kai wannan Manzo -Ya ku waɗanda suka kafirce wa Allah.
🎧 2. {Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba 2}: Ba zan taɓa bautawa duka abinda kuke bautawa ba na gumaka, a yanzu ko a nan gaba.
🎧 3. {Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba 3}: Haka kuma ba za ku zamo masu bauta wa abin da ni na ke bautawa ba, wanda yake shi ne Allah shi kaɗai.
🎧 4. {Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba 4}: Ni kuma ba zan bautawa abinda kuka bauta wa na gumaka ba.
🎧 5. {Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba 5}: Haka kuma ba za ku zamo masu bauta wa abin da ni nake bautawa ba, wanda yake shi ne Allah shi kaɗai.
🎧 6.{Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni 6}: Addinin ku da kuka ƙirƙira yana gareku, ni kuma addini na wanda Allah ya saukar da shi agare ni yana gare ni.
Tambaya ta: 13. Ka ranta Suratul Nasr? kuma ka fassara ta.
Amsa Suratul Nasr da kuma fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Idan taimakon Allah ya zo da buɗi 1. 2. Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, jama'a jama'a 2. 3. To, ka yi Tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne 3}. [Surat Al-Nasr; 1 - 3].
FASSARA:
🎧 1. {Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara 1} Idan taimakon Allah ya zo wa addinin ka - ya kai wannan manzo - da kuma yadda ya ƙarfafi addinin, kuma buɗe Makkah ya faru.
🎧 2. {Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, jama'a jama'a 2}: Kuma ka ga mutane suna shiga addinin musulunci ƙungiya bayan ƙungiya.
🎧 3. {To, ka yi Tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne 3}: Ka sani hakan wata alama ce ta kusancin ƙarewar aikin da aka aiko ka da shi, to sai ka yi Tasbihi haɗi da godewa Ubangijinka, domin gode masa a kan wannan ni'ima ta nasara da kuma buɗe Makkah, kuma ka nemi gafarar sa, lalle shi ya kasance mai yawan karɓar tuba ne yana karɓar tuban bayinsa, kuma yana gafarta musu.
Tabaya ta 11: Karanta Suratul Masad, kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratul Masad da kuma Tafsirin ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Hannãye biyu na Abũlahabi sun taɓe, kuma ya taɓe 1. 2. Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra 2. 3. Zãi shiga wuta mai hũruwa 3. 4. Da kuma matarsa mai ɗaukar iatacen (wuta) 4. 5. A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma) 5}. [Surat Al-Masad: 1 - 5].
FASSARA:
🎧 1. {Hannãye biyu na Abũlahabi sun taɓe, kuma ya taɓe 1}: Hannayan Abu Lahab sun yi asara, wanda yake kuma shi ne baffan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - Abu lahab ɗan Abdul muɗallabi, saboda taɓewar aikin sa, domin ya kasance yana cutar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -, kuma aikin sa ya taɓe.
🎧 2. {Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra 2}: Wane abu ne dukiyar sa da 'ya'yan sa suka tsinana masa? ba su kare shi daga azaba ba, kuma ba su jawo masa rahama ba.
🎧 3. {Zãi shiga wuta mai hũruwa}: Zai shiga wata wuta mai huruwa ranar Al-ƙiyama da zai yi fama da zafin ta.
🎧 4. {Da kuma matarsa mai ɗaukar iatacen (wuta): Kuma da sannu matar sa Ummu Jamil wacce ta kasance ita ma tana cutar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ta hanyar zuba ƙaya akan hanyar sa, zata shiga wutar.
🎧 5. {A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ƙiyãma) 5}: A wuyan ta igiya ce mai ingancin tufkewa za'a koro ta da ita zuwa wuta.
Tambaya ta 15. Ka karanta Suratul Ikhlas kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratul Ikhlas da fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci 1. Allah shi ne abun nufi da bukata 2. 3 Bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba 3. 4. Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi 4}. [Surat Al-Ikhlas: 1 - 4].
FASSARA:
🎧 1. {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci 1} Ka ce: - Ya kai wannan manzo: - Shi ne Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi.
🎧 2. {Allah shi ne abun nufi da buƙata 2} Wato: Shi ne wanda ake ɗaga bukatun halittu zuwa gare shi.
🎧 3 {Bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba 3}: Ba shi da ɗa, tsarki ya tabbata a gare shi, kuma ba shi da uba.
🎧 4. {Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi 4}: Babu kwatankwacin sa a halittar sa.
Tambaya ta: 16. Ka kranta Suratul Falaƙ, kuma ka fassara ta.
Suratut Falak da kuma fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya 1. Daga sharrin abin da Ya halitta 2. Daga sharrin dare, idan ya yi duhu 3. Daga sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri 4. Daga sharrin mai hasada idan ya yi hasada 5}. [Surat Al-falaƙ: 1 - 5].
FASSARA:
🎧 1. {Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya 1}: Ka ce - Ya kai wannan manzo -: Ina neman kariya daga Ubangijin safiya, ina kuma neman tsarin sa.
🎧 2. {Daga sharrin abin da Ya halitta 2}: Daga sharrin abin da zai cuitar daga halittu.
🎧 3. {Da sharrin dare, idan ya yi duhu 3}: Ina neman kariya daga Allah daga sharrikan abin da yake bayyana cikin dare na dabbobi da 'yan fashi.
🎧 4. {Daga sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri 4}: Ina neman kariya daga gare shi daga sharrin matsafa waɗanda suke tofi a guduri (ƙulli).
🎧 5. {Daga sharrin mai hasada idan ya yi hasada 5}: Daga kuma sharrin mai hasada mai ƙiyayya ga mutane, idan yayi musu hassada akan abin da Allah ya ba su na ni'imomin sa, yana son gushewar su daga gare su, da kuma afka cuta da su.
Tambaya ta 17. Karanta Suratun Nas, kuma ka fassara ta.
Amsa: Suratul Nas da fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
{Ka ce: "ina neman tsari ga Ubangijin mutane 1}. Mamallakin mutane 2. Ubangijin Mutane 3. Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa 4. Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane 5. Daga Aljannu da mutane 6}. [Suratun Nas: 1 - 6].
FASSARA:
🎧 1. {Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin mutane 1}: Ka ce - Ya kai wannan manzo -: Ina neman kariya da Ubangijin mutane, kuma ina neman kulawar sa.
🎧 2. {Mamallakin mutane 2}: Wanda Yake tasarriufi acikin su da abin da ya ga dama, ba su da wani mamallaki in ba shi ba.
🎧 3. {Ubangijin Mutane 3}: Abin bautar su da gaskiya, babu wani abin bauta gare su da gaskiya in ba shi ba.
🎧 4. {Daga sharrin mai sanya wasawasi, mai boyewa 4}: Daga sharrin shaiɗan wanda yake jefa waswasin sa ga mutane.
🎧 5. {Wanda yake sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane 5}: Yake jefa wasiwasin sa a zukatan muta ne.
🎧 6. {Daga Aljannu da mutane 6}: Wato: Mai jefa wasawasin yana kasancewa daga cikin mutane kuma yana kasancewa daga cikin Aljannu.
BANGAREN HADISI14
Tambaya ta 1 Ka ƙarasa wannan Hadisin: "Kaɗai dukkanin ayyuka basa tabbata sai da niyyoyi...", kuma ka ambaci fa'idojin sa.
Amsa: An karɓo daga sarkin Muminai baban zaki Umar ɗan Khaɗɗabi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Kaɗai dukkan ayyuka basa tabbata sai da niyyoyi, kuma kowane mutum da irin niyyar da ya niyyata, wanda Hijirar sa ta kasance zuwa ga Allah da Manzon sa to Hijirar sa tana ga Allah da Manzon sa, kuma wanda Hijirar sa takasance dan duniya da zai same ta, ko wata mace da zai aure ta, to Hijirar sa tana ga abinda yayi Hijira zuwa gare shi. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Abinda za'a iya koya daga Hadisin:
1. Kowanne aiki ba makawa gareshi daga niyya, na sallah, da Azumi da Hajji, da wasun su daga ayyuka.
2. Ba makawa daga tsarkakewa acikin niyya ga Allah - maɗaukakin sarki -.
Hadisi Na biyu:
Tambaya ta 2. Ka ƙarasa Hadisin "Wanda ya kago a wannan al'amari namu...", Kuma ka faɗi wasu daga cikin fa'idojin sa.
Amsa: An karɓo daga Uwar muminai Babar Abdullahi A'isha - Allah ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Wanda ya farar acikin al'amarin mu wannan abinda baya daga gare shi to shi abin juyarwane". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Abinda za'a iya koya daga Hadisin:
1. Hani daga ƙirƙira acikin addini.
2. Kuma fararrun ayyuka ababen juyarwa ne ba karɓaɓɓu bane.
Hadisi Na Uku:
Tambaya ta 3. Ka ƙarasa Hadisin: "Wata rana mu muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -..." kuma ka ambaci wasu daga fai'dojin sa.
Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah ya yarda da shi - ya ce: “A yayin da muke zaune tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, yayin da wani mutum ya ɓullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba a ganin alamun tafiya agare shi, kuma babu wani ɗaya daga cikin mu da ya san shi, har sai da ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma ya sanya gwiwowin sa a gwiwoyin sa, ya sanya tafukan sa akan cinyoyin sa, sai ya ce: "Ya Muhammad, ka bani labari game da Musulunci? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Musulunci: Ka shaida cewa babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma lallai Muhammadu Manzon Allah ne, kuma ka tsayar da sallah, ka ba da zakka, ka Azumci Ramadan, kuma ka yi Hajjin ɗaki idan kasami ikon zuwa gare shi". Ya ce: "Ka yi gaskiya", sai mukayi mamakin sa, yana tambayar sa kuma yana gasgata shi. Yace: "To ka bani labari game da imani? Ya ce: "Ka bada gaskiya da Allah, da Mala'ikunsa, da littafan sa, da Manzannin sa, da Ranar Lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara, alherin sa da sharrin sa. Ya ce: "Kayi gaskiya" Yace: "To kabani labari game da kyautatawa". Yace: "Ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa, idan ka kasance ba ka ganin sa, to Shi yana ganin ka". Yace: "Ka bani labari game da Al-ƙiyama". Yace: "Wanda ake tambaya baifi wanda yake tambayar sani ba". Yace: "Ka bani labari game da alamomin ta". Yace: "Kuyanga ta haifi uwargijiyar ta, kuma kaga marasa takalma talakawa masu kiwon dabbobi, suna gasa acikin tsawaita gini'. Sannan ya tafi sai na zauna tsawon lokaci, sannan yace: "Ya Umar, shin kasan mai tambayar?" Na ce: "Allah da Manzonsa ne mafi sani" Yace: "Lallai shine Jibrilu, yazone dan ya sanar daku addinin ku". Muslim ne ya rawaito shi.
Abinda za'a iya koya daga Hadisin:
1. Ka ambaci rukunan Musulunci guda biyar, sune:
Shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu Manzon Allah ne.
Da tsayar da sallah.
Da bayar da zakkah.
Da Azumin watan Ramadan.
Da Hajjin ɗakin Allah mai alfarma.
Ambaton rukunan Imani, su shida ne:
Imani da Allah.
Da Mala'ikun sa.
Da Littattafan sa.
Da Manzannin sa.
Da Ranar Lahira.
Da ƙaddara alherin sa da kuma sharrin sa.
3- Ambaton rukunan kyautatawa, shi rukuni ɗaya ne, shine, ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa, idan ba ka kasance kana ganin sa ba to shi yana ganin ka.
4- Lokacin tashin Al-ƙiyama, babu wanda ya san shi sai Allah maɗaukakin sarki.
Hadisi na Huɗu:
Tambaya ta 4 Ka ƙarasa Hadisin: "Mafi cikar muminai a imani ...", sannan ka ambaci faidojinsa.
Amsa: Daga Abu Huraira - Allah ya yarda dashi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi cikar muminai imani: Mafi cikar su a ɗabi'u". Tirmizine ya ruwaito shi kuma ya ce: "Hadisine kyakykyawa ingantacce".
Abinda za'a iya koya daga Hadisin:
1.Kwaɗaitarwa akan kyawawan halaye.
2. Kuma cikar ɗabi'u yana daga cikin cikar imani.
3. kuma cewa imani yana ƙaruwa kuma yana raguwa.
Hadisi na biyar:
Tambaya ta 5. Ka ƙarasa Hadisin: "Wanda ya rantse da wanin Allah...", kuma ka ambaci wasu daga cikin fa'idojin sa.
Amsa: Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Wanda ya rantse da wanin Allah, to haƙiƙa ya kafirta, ko ya yi shirka". Al-Tirmithi ne yawaito shi.
Abinda za'a iya koya daga Hadisin:
- Rantsuwa bata halatta sai da Allah - maɗaukakin sarki -.
- Rantsuwa da wanin Allah yana daga cikin ƙaramar shirka.
Hadisi na shida:
Tambaya ta 6. Ka ƙarasa Hadisin: "Dayanku bazai yi imani ba har sai na kasance mafisoyiwa a gare shi..." kuma ka ambaci wasu daga cikin faidojin Hadisin.
Amsa: Daga Anas - Allah ya yarda da shi - ya ce: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dayan ku ba zaiyi imani ba har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi daga mahaifin sa da ɗan sa da mutane baki ɗaya". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Daga cikin fa'idojin Hadisin:
-Son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yana wajaba sama da dukkanin mutane.
- Lallai hakan yana daga cikar imani.
Hadisi na bakwai:
Tambaya ta 7. Ka ƙarasa Hadisin: "Dayanku bazaiyi imani ba har sai ya so wa ɗan'uwan sa...', kuma ka ambaci wasu daga cikin faidojin Hadisin.
Amsa; Daga Anas - Allah ya yarda da shi -, ya ce: Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dayanku ba zaiyi imani ba har sai ya sowa ɗan uwan sa abin da yake sowa ga kan sa". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Daga cikin fa'idojin Hadisin:
1. Ya wajaba akan mumini yasowa muminai alheri kamar yadda yake sowa ga kan sa.
- Hakan kuma yana daga cikar imani.
Hadisi na Takwas:
Tambaya ta 8: Ka ƙarasa Hadisin: "Na rantse da wanda raina yake a hannun sa..." sannan ka ambaci faidojin sa.
Amsa: Daga Abu Sa'id - Allah ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunsa!, lallai cewa ita tayi daidai da ɗaya bisa ukun Al-ƙur'ani". Bukhari ne ya rawaito shi.
Daga cikin fa'idojin Hadisin:
1. Falalar Suratul Ikhlas.
2. Cewar ita tayi daidai da ɗaya bisa ukun Al-ƙur'ani.
Hadisi na Tara:
Tambaya ta 9. Ka ƙarasa Hadisin: "Babu dabara babu ƙarfi, sai ga Allah...", kuma ka ambaci wasu daga fa'idojin sa.
Amsa: Daga Abu Musa - Allah ya yarda da shi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu dabara kuma babu ƙarfi, taska ce daga cikin taskokin Aljanna". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Daga cikin fa'idojin Hadisin:
1. Falalar wannan kalmar, kuma ita taska ce daga cikin taskokin Aljanna.
2. Barrantar bawa daga dabarar sa da kuma ƙarfin sa, da dogaron sa ga Allah shi kaɗai.
Hadisi na Goma:
Tambaya ta 10. Ka ƙarasa wannan Hadisin: " Ku sauara, lallai a cikin jiki akwai wata tsoka...", kuma ka ambaci wasu daga cikin fa'idojin sa.
Amsa: Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah ya yarda dasu - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ku saurara, kuma a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, kuma idan ta ɓaci dukkan jiki ya ɓaci". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Daga cikin fa'idojin Hadisin:
1. Gyaran zuciya acikin sa akwai gyaran waje da ciki.
2.Himmatuwa akan gyaran zuciya, domin akwai gyaruwar mutum da shi.
Hadisi na goma sha ɗaya:
Tambaya ta 11. Ka ƙarasa Hadisin: "Wanda ƙarshen maganarsa ta barin duniya ta kasance "La'ilaha illallahui...", kuma ka ambaci wasu daga cikin faidojin sa:
Amsa: Daga Mu'azu ɗan Jabal - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ƙarshen zancen sa ya kasance babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zai shiga Aljanna". Abu Daud ya ruwaito shi.
Daga fa'idojin Hadisin:
1. Falalar : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma bawa zai shiga Aljanna da ita.
2. Da falalar wanda ƙarshen zancen sa na duniya yakasance Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Hadisi na sha biyu:
Tambaya ta 12. Ka ƙarasa Hadisin: "Mumini bai zama mai yawan suka ba, kuma ba mai yawan tsinuwa ba ne..." Da wasu daga cikin faidojin sa.
Amsa: Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mumini bai zama mai yawan sukar mutane ba, kuma ba mai yawan tsinuwa bane, kuma ba mai alfasha bane, kuma ba mai yawan batsa bane". Al-Tirmithi ya ruwaito shi.
Daga cikin fa'idojin Hadisin:
1. Hani daga ɓatacciyar magana da mummuna.
2. Lallai cewa wannan siffar mumini ce a harshen sa.
Hadisi na sha uku:
Tambaya ta 13. Ka ƙarasa wannan Hadisin: "Yana daga kyawun Musuluncin mutum, barin sa abin da babu ruwan sa...", kuma ka ambaci wasu daga fa'idojin sa.
Amsa: Daga Abu Huraira - Allah ya yarda dashi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Yana daga kyawun Musuluncin mutum, barin sa abin da babu ruwan sa". Tirmizi ne ya ruwaito shi da wanin sa.
Daga cikin fa'idojin Hadisin:
1. Barin abinda bai shafi mutum ba, na daga al'amuran addinin wanin sa da kuma duniyar sa.
2. Lalle barin abin da bai shafi mutum ba to yana daga cikar Musuluncin sa.
Hadisi na Sha Huɗu:
Tambaya ta 14. Ka ƙarasa Hadisin : "Wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah...", sannan ka ambaci wasu daga faidojin sa.
Amsa: Daga Abdullahi ɗan Mas'ud: Lalle cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah to yana da kyakykyawan lada, kuma kowane lada za'a ninkashi da tamkarsa goma, bazance: Alif lam meem harafi ɗaya bane, sai dai Ali harafi ne, Meem harafi ne". Al-Tirmithi ya ruwaito shi.
Daga cikin fa'idojin Hadisin:
1. Falalar karanta Al-ƙur'ani.
2. Kuma akan kowanne harafi da ka karanta kana da kyawawan lada da shi.
BANGARAN LADUBBAN MUSULUNCI26
Tambaya ta 1. Ta yaya ladabi zai kasance tare da Allah - maɗaukakin sarki -?
Amsa: 1. Girmama shi - tsarki ya tabbatar masa ya ɗaukaka -.
2. Bauta masa shi kaɗai ba shi da abokin tarayya.
3. Yi ma sa biyayya.
4. Barin saɓa ma sa.
5. Gode ma sa da yaba ma sa - ya girma ya ɗaukaka - akan falalar sa da ni'imomin sa waɗanda ba za su lissafu ba.
6. Yin haƙuri akan abubuwan da ya ƙaddara.
Tambaya ta 1. Ta yaya ladabi zai kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -?
Amsa: 1. Bin sa da kuma koyi da shi.
2. Yi masa biyayya.
3. Barin saɓa ma sa.
4. Gasgata shi a dukkanin abin da ya bada labari.
5. Rashin ƙirƙira acikin ɗari akan sunnar sa.
6. Son sa sama da rai da kuma dukkanin mutane.
7. Girmama shi da taimakon sa da kuma taimakon Sunnar sa.
Tambayata 3. Ya ladabi yake tare da iyaye?
Amsa: 1. Yi wa iyaye biyayya a duk abinda yake ba saɓon Allah bane.
2. Yi wa iyaye hidima.
3. Taimakawa iyaye.
4.Biyan buƙatun iyaye.
5. Yin addu'a ga iyaye.
6. Yin ladabi tare da su a magana, faɗin: "tsaki" baya halatta, shi ne kuwa mafi ƙarancin maganganu.
7. Yin murmushi a fuskar iyaye, kar ka ɗaure fuska.
8. Ba zan ɗaga murya ta ba sama da ta iyaye, zan kuma saurare su, ba kuma zan katse su ba da zance, ba kuma zan kira su da sunan su ba, sai dai zan ce: "Babana", "Babata".
9. Zan nemi izini kafinin shiga ga babana da babata alhali su suna cikin ɗaki.
10. Sumbantar hannu da kan iyaye.
Tambaya ta 4. Yaya zan sadar da zumunci?
Amsa: 1. Ziyartar dangi na kusa, kamar: Dan uwa, da 'yar uwa, da baffa da gwaggo da kawu da inna, da sauran 'yan uwa.
2. Kyautata mu su,ta hanyar magana da aiki da kuma taimaka mu su.
3. Yana cikin haka buga musu waya da kuma tambayar halin da suke ciki.
Tambaya ta:: 5 Ya yakamata in kasance tare da sauran 'yan uwa na da kuma abokaina na?
Amsa: 1. Ina so kuma ina abota da mutanan ƙwarai.
2. Ina nisanta kuma ina barin mutanen banza.
3. Ina yin sallama ga 'yan uwana kuma ina musafaha da su.
4. Ina zuwa gaida su idan ba su da lafiya, kuma ina musu addu'ar samun sauƙi.
5. Ina gaida wanda ya yi atishawa.
6.Ina amsa gayyatar sa idan ya gayyaceni dan ziyartar sa.
7. Ina kuma yi masa nasiha.
8. Ina taimaka ma sa idan aka zalunce shi, ina kuma hana shi yin zalunci.
10.Ina so wa ɗan'uwa na musulmi abin da nake so wa kaina.
11. Ina taimaka masa idan ya buƙaci taimako na.
12. Bazan shafe shi da cuta ba, da magana ko da aiki.
13. Ina ɓoye masa sirrin sa.
14. Ba na zagin sa, kuma ba na gulmar sa. sannan ba na wulaƙanta shi, kuma ba na yi masa hassada, kuma ba na masa binciken ƙwaƙwaf, kuma ba nayi masa maguɗi.
Tambata ta 6. Menene Ladubban Maƙoci?
Amsa: 1. Ina kyautata wa maƙoci ta hanyar magana da aiki, kuma ina taimaka masa idan ya buƙaci taimako na.
2. Ina mishi barka idan yana farin ciki da idi (sallah ƙarama ko babba) ko aure ko ma wanin haka.
3. Ina gaida shi idan ya yi rashin lafiya, kuma ina taya shi alhini idan wata masifa ta afka ma sa.
4. Ina ba shi irin abin cin da nayi gwargwadon iko.
5. Ba na riskar da cuta da shi, da wata magana ko da wani aiki.
6. Ba na damun sa ta ɗaga murya, ko in yi mishi leƙen asiri, kuma ina yin haƙuri da shi.
Tambaya ta 7. Mene ladubban abin cin bako da kuma bakunta?
1. Ina amsa wa duk wanda ya kira ni zuwa baƙuncin sa.
2. Idan ina son in ziyarci wani, ina neman izinin sa da kuma lokacin.
3. Zan nemi izini kafin in shiga.
4. Ba na jinkiri a ziyara.
5. Ina runtse idanu dangane da iyalan gidan.
6. Ina madalla da baƙo kuma ina tarbar shi da kyakkyawa tarba, da sakin fuska, da kyakkyawar magana ta maraba lale.
7. Ina saukar da baƙo a mafi kyawun wuri.
8. Ina kuma girmama shi ta hanyar shirya garar baƙi, na abinci da abin sha.
Tambaya ta 8. Ka ambaci ladubban rashin lafiya, da kuma ziyarar marasa lafiya.
Amsa: 1. A lokacin da nake jin raɗaɗi, ina ɗora hannu na na dama a wurin sa, sai in ce: "Bismillah". Sau uku, sai kuma in ce: "Ina neman tsari da buwayar Allah da kuma ikoin sa (ya kare ni) daga sharrin abinda nake ji, kuma nake tsoro". Sau bakwai.
2. Ina yarda da abinda Allah ya ƙaddara shi, kuma ina haƙuri.
3. Ina gaggawar ziyartar ɗan uwa na mara lafiya, kuma ina ma sa addu'a, ba na tsawaita zama a wurin sa.
3. Ina masa addu'a ba tare da ya nema daga gareni ba.
5. Ina yi masa wasiyya da yin haƙuri da addu'a, da kuma sallah da tsarkaka gwargwadon yanda zai iya.
5.Addu'a ga maralafiya: "Ina roƙon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi maigirma da ya baka lafiya". Sau bakwai.
Tambaya ta 9. Ka ambaci ladubban neman Ilimi.
Amsa: 1. Tsarkake niyya domin Allah - mai girma da ɗaukaka -.
2. Ina aiki da ilimin da nake neman sanin sa.
3. Ina girmama malami, kuma ina mutunta shi a gaban sa da fakuwarsa.
4. Ina zama a gaban sa cikin ladabi.
5. Ina yin shiru gare shi sosai, ba na katse shi a karatun sa.
6.Ina ladabi wurin gabatar da tambaya.
7, Ba na kiran sa da sunan sa.
Tambaya ta 10. Waɗannene ladubban wurin zama?
Amsa: 1. Zan yi sallama ga ma'abota wurin zaman.
2. Ina zama inda wurin zama ya tiƙe da ni, ba zan tayar da wani daga inda yake zaune ba, ko in zauna tsakanin mutane biyu, sai da izinin su.
3. Zan buɗa wuri domin wani na ya ya zauna.
4. Ba zan katse maganar (da ake yi) a wurin zaman ba.
5. Ina neman izini, kuma ina yin sallama kafin juyawa daga wurin zaman.
6. Alokacin da majalisar ta ƙare ina yin addu'ar da ake yi Kaffaratul Majlis. "Tsarki ya tabbatar maKa da godiyar Ka, ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafararKa kuma ina tuba zuwa gareKa".
Tambaya ta 11. Ka ambaci ladubban bacci.
Amsa: 1. Ina bacci da wuri.
2. Ina yin bacci acikin alwala.
3. Ba na bacci rub da ciki.
4. Ina kwanciya a gefa na na dama, sai in sanya hannuna na dama a ƙarƙashin kunci na na dama.
5. Ina karkaɗe shinfiɗa ta.
6.Ina karanta zikiran kwanciya bacci, kamar karanta Ayatul Kursiyy, Suratul Ikhlas, Falaƙi da Nasi. Sau uku Sai in ce: "Da sunanKa Ya Allah nake mutuwa, kuma nake rayuwa".
7. Ina tashi domin yin sallar Asuba.
8. Sai in ce bayan na farka daga bacci: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya matar da mu, kuma taruwa gare shi take".
Tambata ta 12. Menene ladubban abinci?
Amsa:
1. Ina yin niyya a cin abin ci na da shan abin sha na samun ƙarfi akan bautar Allah - mai girma da ɗaukaka -.
2. Wanke hannuwa biyu kafin cin abin ci.
3. Ina cewa: "Da sunan Allah", ina kuma ci ne da hannu na na dama, kuma (ina cin) abinda ke gaba na, ba na ci daga tsakiyar akussa, ko kuma daga gaban wani na.
4. Idan na manta ambaton Allah, sai in ce: "Da sunan Allah a farkon sa da ƙarshen sa".
5. Ina yarda da abinda aka samu na abinci, ba kuma na aibata abinci, idan ya ƙayatar da ni sai in ci shi, idan kuma bai ƙayatar da ni ba sai in bar shi.
6. Ina ci laumoni ne kaɗan, ba na ci da yawa.
7. Ba na busa acikin abin ci ko abin sha, ina barinsa ne har ya huce.
8. Ina taruwa ne da wani na a abin ci, tare da iyali ko baƙo.
9. Ba na fara cin abin ci kafin wani na daga wanda shine mafi girma gare ni.
10. Ina ambaton Allah alokcin da zan sha, kuma ina sha ne a zaune, kuma a kwankwaɗa uku.
11. Ina godewa Allah yayin da na gama daga abincin.
Tambaya ta 13. Ka lissafa ladubban sanya tufafi.
Amsa: 1. Ina fara sanya tufafi na ne ta dama, kuma ina godewa Allah akan hakan.
2. Ba na sakin tufafi har yakai ƙasan idon sawu.
3. 'Ya'ya maza ba sa sanya tufafin 'ya'ya mata, haka kuma 'ya'ya mata ba sa sanya tufafin 'ya'ya maza.
4. Rashin yin kamanceceniya da tufafin kafirai ko fasiƙai.
5.Yin Bisimillah lokacin cire tufafi.
6. Sanya takalmi da (ƙafar) dama a farko, da kuma cirewa da (ƙafar) hagu.
Tambaya ta 14. Ka ambaci ladubban hawa (Abin hawa).
Amsa: 1. Ina faɗin: "Da sunan Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah". {Tsarki ya tabbata ga wanda ya hore mana wannan, alhali kuwa ba mu kasance masu iya rinjaya gare shi ba 13. Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu 14}. [Surat Al- Zukhruf 13-14].
2. Idan na wuce musulmi sai in yi masa sallama.
Tambaya ta 15. Ka ambaci ladubban hanya.
Amsa: 1.Ina daidaituwa kuma ina ƙanƙar da kai a tafiya ta, ina kuma tafiya ne ta daman hanya.
2. Ina yin sallama ga duk wanda na haɗu da shi.
3. Ina rintse idanu na, ba kuma na cutar da kowane ɗaya.
4. Ina yin umarni da kyakkyawan aiki, ina kuma hani daga mummuna.
5. Ina gusar da ƙazanta daga hanya.
Tambaya ta 16. Ka ambaci ladubban shiga gida da kuma fita daga gare shi.
Amsa: 1. Ina fita ne da ƙafa ta ta hagu, sai in ce: "Da sunan Allah, na dogara ga Allah, babu ƙarfi babu dabara sai ga Allah, Ya Allah lallai ni ina neman tsarin Ka akan kada in ɓata ko aɓatar da ni, ko in karkace ko a karkatar da ni, ko in yi zalinci ko a zalince ni, ko in yi wawanci ko a yi wawanci akaina". 2. Ina shiga gida da ƙafa ta ta dama, sai kuma in ce: "Da sunan Allah muka shiga, kuma da sunan Allah muka fita, kuma ga Allah Ubangijin mu muka dogara".
3. Ina farawa da yin asuwaki, sannan in yi sallama ga masu gida.
Tambaya ta 17. Ka ambaci ladubban biyan buƙata.
Amsa: 1. Ina shiga ne da ƙafa ta ta hagu.
2. Sai in ce kafin shiga: "Da sunan Allah, Ya Allah lallai ni ina neman tsarin Ka daga shaiɗanu maza da shaiɗanu mata".
3. Ba na shiga da wani abun da yake akwai ambaton Allah acikin sa.
4. Ina ɓoyuwa a halin biyan buƙata.
5. Ba na magana a wurin da biyan buƙata.
6.Ba na fuskantar Al-ƙibla, kuma ba na juya mata baya, a yayin fitsari ko bayan gida.
7. Ina amfani da hannu na na hagu a kawar da najasa, ba na amfani da na dama.
8. Ba na biyan buƙata ta akan hanyar mutane ko kuma inuwar su.
9. Ina wanke hannu na bayan biyan buƙata.
10. Ina fita ne da ƙafa ta ta hagu, sai kuma in ce: "Ina neman gafarar Ka".
Tambaya ta 18. Ka ambaci ladubban masallaci.
Amsa:1. Ina shiga masallaci ne da ƙafa ta ta dama, sai in ce: "Da Sunan Allah, Ya Allah Ka buɗa min ƙofofin rahamar Ka".
2. Ba na zama har sai na yi sallah raka'a biyu.
3. Ba na wuce wa ta gaban mai sallah, ko kuma in yi cigiyar ɓataccen abu acikin masallaci, ko in sayar ko kuma in saya a cikin masallaci.
4. Ina fita daga masallaci da ƙafa ta ta hagu, sai in ce: "Ya Allah, lallai ni ina roƙon Ka daga falalar Ka".
Tambaya ta 19. Ka ambaci ladubban sallama.
Amsa: 1. Alokacin da na haɗu da wani musulmi zan fara yi masa sallama, da faɗin: "Amincin Allah da rahamar Sa da kuma albarka Sa su tabbata a gare ku". ba da wanin sallama ba, bana nuni da hannu na shi kaɗai.
2. Ina yin murmushi a fuskar duk wanda nakewa sallama.
3. Kuma ina yin musafaha da shi da hannu na na dama.
4.Idan wani ɗaya ya gaishe ni da gaisuwa, to ni ma zan gaishe shi da mafi kyau daga gare ta, ko na mayar da tamkar ta.
5. Ba na fara yi wa kafiri sallama, idan ya yi sallama zan mayar masa da tamkar ta.
6. Kuma ƙarami yake fara yi wa babba sallama, wanda ke kan abin hawa shi zai fara yi wa mai tafiya a ƙasa sallama, wanda ke tafiya a ƙafa shi zai fara yi wa na zaune sallama, mutane kaɗan su za su fara yi wa masu yawa sallama.
Tambaya ta 20. Ka ambaci ladubban neman izini.
Amsa: Ina neman izini kafin shiga wuri.
2. Ina neman izini sau uku, bana ƙarawa, bayan su sai in juya.
3, Ina ƙwanƙwasa kofa a hankali, ba na tsayawa a gaban ƙofa, kai a daman ta ne ko a hagun ta.
4. Ba na shiga ga baba na ko baba ta ko ɗaya daga ɗakunan kafin neman izini, musamman ma kafin Asuba, da lokacin baccin rana, da kuma bayan sallar Isha'i.
5. Zai iya yiwuwa na shiga wuraran da ba na zama ba, kamar: Asibiti, ko wurin kasuwanci ba tare da neman izini ba.
Tambaya ta 21. Ka ambaci ladubban tausayawa dabbobi.
Amsa: 1. Ina ciyar da dabbobi kuma ina shayar da su.
2. Jin ƙai da tausayi ga dabbobi, da rashin ɗora musu abin da ba za su iya ba.
3. Ba na azabtar da dabbobi da kowanne irin nau'i na azaba, da cutarwa.
Tambaya ta 22. Ka ambaci ladubban motsa jiki.
Amsa: 1. Ina niyyar samun ƙarfi saboda bautar Allah da kuma yardar Shi da motsa jiki.
2. Ba ma yin wasa a lokacin sallah.
3. Yara maza ba sa wasan motsa jiki tare yara mata.
4. Ina sanya kayan motsa jiki na wanda zai rufe mini al'aura ta.
5. Ina nisantar wasannin motsa jikin da aka haramta, kamar waɗanda acikin su akwai marin fuska, ko yaye al'aurori.
Tambaya ta 22. Ka ambaci wasu daga ladubban kakaci:
Amsa: 1.Gaskiya a kakaci da rashin ƙarya.
2. Kakaci wanda ya kaɗaita daga izgili da wulaƙanci da cutarwa da tsoratarwa.
3. Rashin yawaita kakaci.
Tambaya ta 24. Lissafa ladubban atishawa.
Amsa: 1. Sanya hannu ko tufafi ko hankici yayin atishawa.
2. Ka godewa Allah bayan atishawa (ka ce): "Godiya ta tabbata ga Allah".
3. Sai ɗan'uwan sa ko abokin sa ya ce da shi: "Allah Ya yi maka rahama".
4. Idan ya faɗa masa: sai ya ce: "Allah Ya shiryar da ku, kuma Ya kyautata sha'anin ku".
Tambata ta 25. Menene ladubban hamma?
Amsa: 1. Koƙari wurin matse hammar.
2. Rashin ɗaga murya da faɗin: "hah, ha".
3. Sanya hannu a baki.
Tambaya ta 26. Ka ambaci laddubban karatun Al-ƙur'ani.
Amsa: 1. Yin karatun da tsarki bayan alwala.
2. Zama da Ladabi da natsuwa.
3. Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗani a farkon karatu.
4. Ina jujjuya ma'anonin karatun.
BANGAREN DABI'U:30
Tambaya ta 1. Ka ambaci falalar kyawawan ɗabi'u.
Amsa: Annabi - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi cikar muminai imani mafi kyawunsu a ɗabi'u". Tirmizi da Ahmad ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 2. Saboda me muke lizimtar ɗabi'un Musulunci?
Amsa: 1. Domin cewa su sababi ne na soyayyar Allah - maɗaukakin sarki -.
2. Kuma sababi ne na soyayyar halitta.
3. Kuma su ne mafi girma a ma'auni.
4. Kuma ana ninka lada da sakamako saboda kyawawan ɗabi'u.
5.Kuma alama ce ta cikar imani.
Tambaya ta 3. Daga ina zamu ɗakko ɗabi'u?
Amsa: Daga Al-ƙur'ani mai girma, Allah - maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lallai wannan Al-ƙur'anin yana shiryarwa ga (halaye) waɗanda suke mafi daidaita}. [Surat Al-Isra'i: 9]. Daga Sunna ta Annabi kuma: inda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Kaɗai ni an aiko ni ne don in cika kyawawan ɗabi'u". Ahmad ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 4. Menene ɗabi'u na kyautatawa da surorinsa?
Amsa: Kyautatawa: Shi ne jin tsoron Allah a koda yaushe, da kuma shinfiɗa alheri da kyautatawa ga halittu.
Annabi - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Lallai Allah ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu". Muslim ne ya ruwaito shi.
Daga cikin nau'ukan kyautatawa :
- Kyatatawa acikin bautar Allah - maɗaukakin sarki - ta hanyar tsarkake niyya acikin bautar sa.
- Kyautatawa ga mahaifa, ta hanyar faɗa da kuma aikatawa.
- kyautatawa ga zumunci da 'yan uwa.
- Kyautatawa ga maƙoci.
- Kyautatawa ga marayu da miskinai.
- Kyautatawa ga wanda ya munana maka.
- Kyautatawa a zance.
- Kyautatawa a tattaunawa.
- Kyautatawa ga dabbobi.
Tambaya ta 5. Menene kishiyar kyautatawa?
Amsa: Kishiyar kyautatawa ita ce munanawa.
* Yana daga haka: Barin tsarkake niyya acikin bautar Allah - maɗaukakin sarki -.
* Da saɓawa iyaye.
* Da yanke zumunci.
* Da mummunar maƙwabtaka.
* Da barin kyautatawa zuwa ga talakawa da miskinai da wanin wannan, na abinda ya shafi munanan maganganu da kuma ayyuka.
Tambaya ta 6. Waɗanne ne nau'ukan amana, kuma da surorinsu?
Amsa:
1. Amana acikin kiyaye haƙƙoƙin Allah - maɗaukakin sarki -.
Surorinsu: Amana acikin yin ibadu na abinda ya shafi Sallah, da Zakkah, da Azimi, da Hajji, da kuma waninsu, na daga abinda Allah Ya wajabta akan mu.
2.Amana a cikin kiyaye haƙƙoƙin halittu:
- Daga abinda ya shafi kiyaye mutuncin mutane.
- Da dukiyoyin su.
- Da jinanan su.
- Da sirrikan su, da dukkan abinda mutane suka amintar da kai akan sa.
Allah - maɗaukakin sarki - Ya faɗa acikin ambatan siffofin masu rabauta. {Sune waɗannan da suke ga amãnõninsu da alƙawarinsu mãsu tsarẽwa ne}. [Surat: Al-Mu'uminun: 8].
Tambaya ta 7. Mecece kishiyar amana?
Amsa: Ha'inci, shi ne tozarta haƙƙoƙin Allah - maɗaukain sarki -da kuma haƙƙoƙin mutane.
Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Alamomin munafiki uku ne"- A ciki sai ya ambaci: "Idan aka amince masa sai ya yi ha'inci". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi).
Tambaya ta 8. Wanne ne ɗabi'ar gaskiya?
Amsa: Shi ne bayar da labari da abinda yake ya yi daidai da yadda abin yake, ko kuma abin akan yanda yake.
Daga surorinsa:
Gaskiya acikin zance da mutane.
Gaskiya acikin alƙawari.
Gaskiya akowacce magana da kuma kowanne aiki.
Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Lallai gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma lallai mutum zai yi gaskiya har ya kasance cikakken mai gaskiya". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi).
Tambaya ta 9. Mece ce kishiyar gaskiya?
Amsa: Karya. Ita ce kuma saɓanin haƙiƙa, daga wannan: Yi wa mutane ƙarya, da saɓawa alƙawaruka, da shaidar ƙarya (zur).
Annabi - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai ƙarya tana shiryarwa zuwa fajirci, kuma lallai fajirci yana shiryarwa zuwa wuta, lallai mutum zai dinga yin ƙarya har sai an rubuta shi cikakken maƙaryaci a wurin Allah". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi). Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: ("Alamomin munafiki uku ne" sai ya ambata daga ciki: "Idan ya bada labari sai ya yi ƙarya, kuma idan ya yi alƙawari ya saɓa". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi).
Tambaya ta 10. Ka ambaci nau'ukan ƙakuri:
Amsa: Haƙuri akan bautar Allah - maɗaukakin sarki -.
- Haƙuri akan ƙin yin saɓo.
- Haƙuri akan abubuwan da Allah ya ƙaddara masu raɗaɗi, da kuma godewa Allah akowanne hali.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Allah Yana son masu haƙuri 146}. [Surat Aal Imran: 146]. Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: ’’Mamaki ga lamarin mumini, lallai al'amuran sa dukkannin su alheri ne, wannan bai zamo ga wani ɗaya ba sai mumini, idan farin ciki ya same shi sai yayi godiya, sai ya zama alheri gare shi, idan kuma cuta ta same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zama alheri a gare shi". Muslim ne ya rawaito shi.
Tambaya ta 11. Menene kishiyar haƙuri?
Amsa: Shine rashin yin haƙuri akan biyayya ga Allah, da kuma rashin yin haƙuri akan saɓawa Allah, da yin fushi akan abubuwan da Allah ya ƙaddara, ta hanyar maganganu da kuma ayyuka.
Daga cikin surorinsa:
$ Burin mutuwa.
$ Marin kundukuki.
$ Yaga tufafi.
$ Fizgar gasu.
$ Yi wa kai mummunar addu'a ta halaka.
Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Sakamako yana tare da girman bala'i, kuma lallai cewa Allah idan Ya so wasu mutane to sai ya Jarrabesu, wanda ya yarda (da Jarrabawar) to yardar tana gareshi, wanda kuma yayi fushi to fushin yana gareshi". Tirmizi da Ibn Majah ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 12. Ka ambaci ɗabi'un taimakekeniya.
Amsa: Shi ne taimakon da mutane za su yi a taskanin su akan gaskiya da alheri.
Surorin taimakekeniya:
oTaimakekeniya acikin mayar da haƙƙoƙi.
o Taimakekeniya acikin juyar da azzalimi.
o Taimakekeniya acikin toshe buƙatun mutane da miskinai.
o Taimakekeniya akan kowanne alheri.
o Rashin taimakekeniya akan aikata laifi da cuta da shishshigi.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ku yi taimakekeniya akan aikin alheri da kuma tsoron Allah, kada kuyi taimakekeniya akan laifi da shishshigi, kuji tsoron Allah, lallai Allah mai tsananin uƙuba ne 2}. [Surat Al-Ma'idah: 2]. Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Mumini ga mumini tamkar gini ne, sashin sa yana ƙarfafar sashi". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi). Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalunce shi, kuma kada ya miƙa shi, wanda ya kasance acikin buƙatar ɗan uwan sa Allah zai kasance acikin buƙatar sa, wanda ya yaye wani baƙin ciki daga musulmi Allah zai yaye wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin ranar Al-ƙiyama daga gareshi, wanda ya suturta wani musulmi Allah zai suturta shi ranar Al-ƙiyama". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi).
Tambaya ta 13. Waɗanne ne nau'ukan ɗabi;un kunya?
Amsa: 1. Jin kunyar Allah: Yana kasancewane ta hanyar kada ka saɓa masa - tsarki ya tabbatar masa -.
2. Jin kunyar mutane: Daga wannan akwai barin zance na alfasha mummuna da kuma yaye al'aura.
Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Imani saba'in da wani abune" - ko: "Sittin da wani abune" - "Yanki, mafi ɗaukakar su: faɗin: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, mafi ƙasƙantar su; Gusar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani yankine na imani". Muslim ne ya rawaito shi.
Tambaya ta 14. Ka ambaci ɗ abi'un surorin tausayi.
Amsa: - Tausayawa masu manyan shekaru, da kuma girmama su.
- Tausayawa masu ƙananan shekaru da kuma ƙananan yara.
- Tausayawa talaka da miskini da mabuƙaci.
- Tausayawa dabbobi shine ka ciyar da su, kuma kada a cutar da su.
Daga wannan faɗin Annabi - tsira da amici su tabbata agareshi -: "Kana ganin muminai a cikin jin ƙan su da soyayyr su kamar jiki ne, idan wata gaɓa ta koka, sai duka jikin ya ɗauka da rashin bacci da kuma zazzaɓi". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi). Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Masu jin ƙai Allah yana jin ƙan su, ku ji ƙan waɗanda ke bayan ƙasa sai wanda yake sama ya ji ƙan ku". Abu Daud da Al-Tirmizi ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 15. Waɗanne ne nau'ukan ɗabi'ar soyayya?
Amsa: Son Allah - maɗaukakin sarki -.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma waɗanda suka yi imani sune mafi tsananin soyayya ga Allah}. [Surat Al-Baƙarah: 165].
Son Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannun Sa, ɗayan ku ba zaiyi imani ba har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi daga mahaifin sa da kuma ɗan sa". Bukhari ne ya rawaito shi.
Son Muminai, da kuma son alheri gare su kamar yadda kake so wa kanka.
Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Dayanku ba zaiyi imani ba har sai ya sowa ɗan uwansa abin da yake sowa kan sa". Bukhari ne ya rawaito shi.
Tambaya ta 16. Ka faɗi ma'anar walwala.
Amsa: Ita ce sakin fuska, tare da farin ciki da murmushi da tausasawa, da bayyanar da farin ciki a lokcin haɗuwa da mutane.
Ita ce kuma kishiyar ɗaure fuska a fuskar mutane daga abinda zai kore su.
Acikin falalaR hakan hadisai da yawa sun zo, daga Abu Zarr - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ni: "Kada ku wulaƙanta wani abu daga aikin alheri, koda kuwa ka haɗu da ɗan'uwan ka ne da sakakkiyar fuska". Muslim ne ya rawaito shi. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Murmushin ka a fuskar ɗan'uwan ka sadaka ne". Al-TirmiZi ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 17. Mecece Hassada?
Amsa: Ita ce fatan gushewar ni'ima daga wani, ko kuma ƙyamar ni'ima ga wani.
Allah - maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma daga sharrin mai hassada idan ya yi hassada 5}. [Suratu Falaƙ: 5].
Daga Anas ɗan Malik - Allah ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku ƙi juna, kada ku yiwa juna hassada, kada ku juyawa juna baya, ku kasance - yaku bayin Allah - 'yan'uwan juna. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 18. Menene Izgili?
Amsa: Shine izgili ga ɗan'uwan ka musulmi, da wulaƙantar da shi, wannan baya halatta.
Allah - maɗaukakin sarki - Ya ce dangane da hani daga hakan: {Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasance mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibata kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsiƙanci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai 11}. [Suratul Hujurat: 11].
Tambaya ta 19. Kayi bayani akan ƙanƙar da kai.
Amsa: Shi ne kada mutum ya ga kan sa (mafifici) akan mutane, kada ya wulaƙanta mutane, kada kuma yaƙi gaskiya.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma bayin Mai rahama su ne waɗanda suke tafiya a bayan ƙasa cikin sauƙi}. [Suratul Furƙan: 62]. Wato: Masu ƙanƙar da kai. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kuma wani ɗaya bazai ƙankar da kai ga Allah ba face sai Allah ya ɗaukaka shi". Muslim ne ya ruwaito shi. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah ya yi wahayi zuwa gareni cewa ku ƙanƙar da kanku, ta yadda babu wani ɗaya da zai yi alfahari a kan wani ɗaya, kuma kada wani ɗaya ya yi zalinci akan wani ɗaya". Muslim ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 20.Waɗanne ne nau'ukan girman kai ababen haramtawa?
Amsa: 1. Girman kai akan gaskiya, shi ne ƙin karɓar gaskiya da rashin karɓar ta.
2. Girman kai ga mutane, shi ne, shi ne wulaƙantar da su, da maida su ba ba'abakin komai ba.
Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Ba zai shiga Aljanna ba wanda duk ya kasance akwai kwatankwacin ƙwayar zarra na girman kai acikin zuciyar sa". Sai wani mutum ya ce: Lallle mutum yana son tufafin sa ya kasance mai kyau, takalmin sa ya kasance mai kyau? Sai ya ce: "Lallai Allah mai kyau ne, kuma yana son kyau. Girman kai shi ne ƙin gaskiya da wulakanta mutane". Muslim ne ya rawaito shi.
- Kin gaskiya: Dawo da ita.
- Wulaƙanta mutane: Wulaƙanta su.
- Tufafi mai kyau, da takalmi mai kyau basa cikin girman kai.
Tambaya ta 21. Ka ambaci wasu daga nau'ukan algus abin haramtawa.
Amsa: - Algus a siye da siyarwa, shi ne ɓoye aibin dake jikin haja (Abin siyarwa).
- Algusu a neman ilimi, misalin wannan algusun da ɗalibai suke yi acikin jarabawa.
- Algus a magana, kamar shaidar ƙarya (shaidar zur).
- Kin cika alƙawari da abinda kake faɗa, da kuma abinda kake ittifaƙi dashi tare da mutane.
Acikin hani daga algus, lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya wuce wani shuri na abinci, sai ya sanya hannun sa acikin sa, sai 'yan yatsun sa suka samu danshi, sai ya ce: " Menene wannan ya kai mai wannan abincin? Sai ya ce: Ai ruwan sama ne ya zuba acikin su ya Ma'aikin Allah, sai ya ce: "Shin ba ka sanya shi a saman abin cin ba, domin mutane su gan shi? Duk wanda ya yimana algus to baya tare da ni". Muslim ne ya rawaito shi.
Subrah: Shi ne shuri na abinci.
Tambaya ta 22. Mecece gulma?
Amsa: Itace ambaton ɗan'uwanka musulmi da abinda ba yake ƙi, alhali ba ya nan.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma kada sashinku ya yi gulmar sashi, shin ɗayan ku zai so ya ci naman ɗan'uwan sa a mace, to kun ƙi shi, ku ji tsoron Allah, lallai Allah Mai yawan karɓar tuba ne kuma Mai jin ƙai ne 12}. [Suratul Hujurat: 12].
Tambaya ta 23. Ka faɗi ma'anar annamimanci.
Amsa: Shi ne ɗaukar zantuttuka tsakanin mutane, domin ɓatawa tsakanin su.
Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Mai annamimanci ba zai shiga Aljanna ba". Muslim ne ya rawaito shi.
Tambaya ta: 24. Mecece kasala?
Amsa: Ita ce jin nauyin aikata alheri, da duk abinda aikata shi ya wajaba akan mutum.
Yana daga wannan: Kasala acikin aikata wajibai.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lalle ne munãfukai sunã yaudarar Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga sallah, sai su tãshi sunã mãsu kasãla, suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan}. [Surat Al-Nisa'i: 142].
To yana kamata ga mumini ya bar kasala da sanyin jiki da son zama, (yayi ƙoƙari) a tafiya acikin aiki da kazar-kazar da ƙoƙari da dagewa a wannan rayuwa da abinda zai yardar da Allah - Maɗaukakin sarki -.
Tambaya ta25. Ka ambaci na'ukan fushi.
Amsa: 1. Fushi abin yabo: Shi ne kuwa ya kasance domin Allah, idan kafIrai ko munafukai ko wasun su suka keta alfarmar Allah - tsarki ya tabbatar masa -.
2. Fushi abin zargi: Shi ne fushin da zai sanya mutum ya aikata ko ya faɗi abinda baya kamata.
Maganin fushi abin zargi.
Yin alwala.
Zama, idan ya kasance a tsaye yake, da kuma kwanciya idan ya kasance a zaune yake.
Ya lazimci wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - acikin wannan: "Kada ka yi fushi".
Ya riƙe ran sa daga afkawa wani abu ayayin fushin.
Neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa.
Yin shiru.
Tambaya ta 26.Menene leƙen asiri?
Amsa: Shi ne leƙe da bincikar al'aurorin mutane da abinda suke ɓoye shi (ba sa so a gani).
Daga cikin surorin sa waɗanda aka haramta:
- Tsinkaya akan al'aurorin mutane acikin gidaje.
- Neman jin mutum zuwa zancen wasu mutane ba tare da sanin su ba.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kada ku yi binciken ƙwaƙwaf...}. [Suratul Hujurat: 12].
Tambaya ta 27. Mece ce ɓarna? kuma menene rowa? kuma menene karamci?
Amsa: Barna ita ce kashe dukiya ba tare da haƙƙinta ba.
Kishiyarsa: Rowa: Ita ce kamewa daga haƙƙinta.
Abinda yake daidai shi ne kasantuwa tsaka-tsakiya tsakaninsu, kuma musulmi ya kasance mai karamci ne.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa}. [Suratul Furƙan: 67].
Tambaya ta 28. Menen tsoro?, kuma mecece gwarzantaka?
Tsoro: Shi ne ya ji tsoron abinda bai kamata ya ji tsoronsa ba.
Misalin jin tsoro daga faɗin gaskiya, da kuma hana mummunan abu.
Gwarzantaka: Ita ce gabatowa akan gaskiya, wannan kamar gabatowa a fagagen fama domin kare Musulunci da musulmai.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya kasance yana faɗa acikin a addu'ar sa: "Ya Ubangiji ina neman tsarin Ka daga tsoro". Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: “Karfaffan mumini ya fi alheri da soyuwa a wurin Allah daga Mumini rarrauna, a kowanne akwai Alheri”. Muslim ne ya rawaito shi.
Tambaya ta 29. Ka ambaci wasu daga maganganun harshen da aka haramta su.
Amsa: Misalin tsinuwa da zagi.
- Da kuma misalin faɗin wane: "dabba", ko ire-irensu daga lafuzza.
- ko ambaton al'aurori daga kalmomin alfasha da muni.
- Haƙiƙa Annabi - tsirada amincin Allah su tabbata agareshi - yayi hani daga wannan gaba ɗayansa, sai ya ce: "Mumini ba mai yawan sukar mutane bane, kuma ba mai yawan tsinuwa bane, ba kuma mai batsa bane, haka ba ya mummunar magana". Al-Tirmizi da Ibn Hibban ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 30. Ka ambaci sabubban da za su taimakawa musulumi akan siffantuwa da kyawawan ɗabi'u.
Amsa: 1. Addu'a akan Allah ya azurta ka da kyawawan ɗabi'u, ya kuma taimaka maka akan haka.
2.Jin tsoron Allah - mai girma da ɗaukaka -, da cewa shi Yana sane da kai, Yana kuma jin ka, Yana ganin ka.
3. Tuna ladan kyawawan ɗabi'u, da kuma cewa su sababi ne na shiga Aljanna.
4. Tuna mummunar makoma ta munanan ɗabi'u, kuma cewa su sababi ne na shiga wuta.
5. Kuma su kyawawan ɗabi'u suna janyo soyayyar Allah da soyayyar halittar sa. Kuma su munanan ɗabi'u suna janyo fushin Allah da kuma fushin halittar Sa.
6. Karanta tarihin Annabi - tsira da aminci su tabbata a gare shi - da kuma koyi da shi.
7. Abota da mutanan kirki, da kuma nisantar mutanan banza.
BANGAREN ADDU'OI DA ZIKIRI43
Tambaya ta: 1. Menene falalar zikiri?
Amsa: Annabi - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Misalin wanda yake ambaton Ubangijin sa, da wanda ba ya ambaton Ubangijin sa, kamar rayayye ne da mataccce". Bukhari ne ya rawaito shi.
- Wannan kenan؛ domin darajar rayuwar mutum (tana tabbata ne) da gwargwadon ambaton sa ga Allah - maɗaukakin sarki -.
Tambaya ta 2. Ka ambaci waɗansu daga a'idojin zikiri.
Amsa: 1. Yana kawo yardar Mai Rahama.
2. Yana korar Shaiɗan.
3. Yana kare musulmi daga saharruka.
4. Lada da sakamako suna tabbata ta dalilin sa.
Tambaya ta 3. Menene mafificin zikiri?
Amsa: "Babu abIn bautawa da gaskiya sai Allah". Al-Tirmizi da Ibnu Majah ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta:4 Me kake faɗa yayin tashi daga bacci?
Amsa: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya rayar da mu bayan Ya matar da mu, kuma taruwa tana gare Shi". An haɗu akan sa (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Tambaya ta 5. Mekake faɗa idan ka sanya tufafin ka?
Amsa: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya tufatar da ni wannan tufafin kuma ya azurtani shi, ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba". Abu Daud da Al-Tirmizi ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 6. Me kake faɗa idan ka cire tufafin ka?
Amsa: "Da sunan Allah". Al-Tirmizi ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 7. Mecece addu'ar sanya sabon tufafi?
Amsa: "Ya Allah, godiya ta tabbata gare Ka, kai ne ka tufatarda ni shi, ina roƙon Ka alherin sa da alherin abinda akayi domin sa, ina kuma neman tsarin Ka daga sharrin sa, da kuma sharin abinda akayi domin sa". Abu Daud da Al-Tirmizi ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 8. Mecece addu'a ga wanda ya sanya sabon tufafi?
Amsa: Idan ka ga sabon tufafi ga waninka sai kayi masa addu'a, ka ce: " (Fatan Allah ) yasa ka tsufantar da ita, kuma Allah - maɗaukakin sarki - Ya canza ma ka (wata)". Abu Daud ne ya ruwaito shi.
Tambaya 9. Ka ambaci addu'ar shiga banɗaki, shine wurin biyan buƙata.
"Ya Allah lallai ni ina neman tsarin Ka daga shaiɗanu maza da shaiɗanu mata". An haɗu akan sa (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Tambaya ta 10. Mecece addu'ar fitowa daga banɗaki?
Amsa: "Ina neman gafarar Ka". Abu Daud da Al-Tirmizine suka ruwaito shi.
Tambaya ta 11. Me kake cewa kafin ka fara alwala?
Amsa: "Da sunan Allah". Abu Daud da waninsa ne suka ruwaitoshi.
Tambaya ta 12. Wanne ne zikirin da ake yi bayan gama alwala?
"Ina shida cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, bashi da abokin tarayya, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammad bawan Sa ne kuma Manzon Sa ne". Muslim ne ya rawaito shi.
Tambaya ta 13. Wane zikiri ne yayin fita daga masauki?
Amsa: "Da sunan Allah, na dogara ga Allah, babu dabara, babu ƙarfi sai ga Allah". Abu Daud da Al-Tirmizine suka ruwaito shi.
Tambaya ta 14. Wane zikiri ne yayin shiga gida?
Amsa: "Da sunan Allah muka shiga, da kuma sunan Allah muka fita, kuma ga Allah Ubangijin Mu muka dogara, sannan yayi sallama ga iyalan sa". Abu Daud ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 15. Me cece addu'ar shiaga masallaci?
Amsa: "Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamar Ka". Muslim ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 16. Ka ambaci addu'ar fita daga masallaci?
Amsa: "Ya Allah ina roƙon Ka daga falalar Ka". Muslim ne ya ruwaito shi.
Tmabaya ta :17. Me kake faɗa yayin jin kiran sallah?
Amsa: Ina faɗin abinda mai kiran sallar yake faɗa, sai dai a: "Kuyi gaggawa zuwa ga sallah". Da kuma "Kuyi gaggawa zuwa ga tsira". Sai in ce: "Babu dabara kuma babu ƙarfi sai ga Allah". An haɗu akansa (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).
Tambaya ta 18. Me kake faɗa bayan kiran sallah?
Amsa: "Kana yin sallati ne ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Muslim ne ya ruwaito shi. Kuma sai ka ce: "Ya Allah ma'abocin wannan cikakkiyar addu'a, da sallah mai tsayawa, Ka baiwa (Annabi) Muhammad Wasila (Matsayine a Aljanna) da fifiko, Ka tayar da shi wani matsayi abin yabo, wanda Ka yi alƙawarin sa". Bukhari ne ya ruwaito shi.
Sai ka yi addu'a tsakanin kiran sallah da kuma iƙama, domin addu'a (awannan lokacin) ba'a dawo da ita.
Tambaya ta 19. Me kake faɗa da safe da kuma yamma na zikirai?
Amsa. 1. Ina karanta Ayatul Kursiyyu: {Allah, bãbu wani abin bautawa da gaskiya fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, ballantana barci, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma}. [Surat Al-Baƙara: 255]. 2. Ina kuma karanta: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin ƙai. 1. {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci 1. Alla shi ne abun nufi da Buƙata 2. 3 Bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba 3. 4. Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi 4}. Kafa uku. Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. 1. {Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya 1. Daga sharrin abin da Ya halitta 2. Daga sharrin dare, idan ya yi duhu 3. Daga sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri 4. Daga sharrin mai hasada idan ya yi hasada 5}. Kafa uku. Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. {Ka ce: "ina neman tsari ga Ubangijin mutane 1}. Mamallakin mutane 2. Ubangijin Mutane 3. Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa 4. Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane 5. Daga Aljannu da mutane 6}. Kafa uku. 3. "Ya Allah kaine Ubangijina babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Ka halicceni kuma nine bawan Ka, kuma ni ina kan alƙawarin Ka da wuyayen Ka iya iyawata, ina neman tsarin Ka daga sharrin abinda na aikata, ina iƙirari da ni'imar Ka gareni, kuma ina iƙirari da zunubi na, to ka gafarta mi ni, cewa shi ba mai gafarta zunubai sai Kai". Bukhari ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 20. Me kake cewa lokacin kwanciya bacci?
Amsa: "Da sunan Ka ya Allah nake mutuwa kuma nake rayuwa". An haɗu akan sa (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Tambaya ta 21. Me kake cewa kafin cin abin ci?
Amsa: "Da sunan Allah".
To idan ka manta a farko, sai ka ce:
"Da sunan Allah a farkon sa da kuma ƙarshen sa". Abu Daud da Al-Tirmizi ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta:22 Me kake faɗa yayin gama cin abin ci?
Amsa: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da ni wannan, kuma ya azurtani shi, ba tare da wata dabara daga gare ni ko ƙarfi ba". Abu Dawud da Ibnu Majah da wasun su ne suka ruwaitoshi.
Tambaya ta 22. Mecece addu'ar baƙo ga mai abin ci?
Amsa: "Ya Allah ka sanya musu albarka a abinda ka azurta su da shi, ka kuma gafarta musu ka yi musu rahama". Muslim ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 24. Me mutum yake cewa idan ya yi atishawa?
Amsa: "Godiya ta tabbata ga Allah".
Kuma ɗan'uwan sa ko abokin sa ya ce da shi: "Allah Ya yi maka rahama".
4. Idan ya faɗa masa: sai ya ce: "Allah Ya shiryar da ku, kuma Ya kyautata sha'aninku". Bukhari ne ya ruwaito shi.
Tamabaya ta 25. Me kake cewa lokacin ta shi, da kuma gamawa daga mazauni?"Addu'ar kaffarar wurin zama".
"Tsarki ya tabbatar maKa da godiyar Ka, ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafarar Ka kuma ina tuba zuwa gare Ka". Abu Daud da Tirmizi da wasun su ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 26. Mecece addu'ar hawa abin hawa?
Amsa: Da sunan Allah, godiya ta tabbata ga Allah. {Tsarki ya tabbata ga wanda Ya hore mana wannan, kuma mu bamu kasance muna da rinjaye gareshiba 14}, "Godiya ta tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, tsarki ya tabbata gare Ka, ya Allah lallai ni na zalinci kaina, to Ka gafarta mini, domin babu mai gafarta zunubai sai Kai". Abu Daud da Al-Tirmizi ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 27. Ka ambaci addu'ar tafiya?
Amsa: "Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma {Tsarki ya tabbata ga wanda ya hore mana wannan, kuma mu bamu kasance muna da rinjaye gareshiba 14}. Ya Allah lallai muna roƙan Ka a wannan tafiya tamu ayyukan ƙwarai da tsoron Ka, daga aiki kuma wanda Kake yarda (Dashi). Ya Allah Ka sawwaƙe mana wannan tafiya tamu, Ka naɗe mana tsawonta. Ya Allah Kai ne ma'aboci a wannan tafiya, kuma halifan mu a iyalan mu. Ya Allah lallai muna neman tsarin Ka daga wahalhalun tafiya, da kuma mugun gani, da mummunar makoma a dukiya da iyali".
Idan kuma ya dawo sai ya faɗesu, ya kuma ƙara:
"Muna masu dawowa, masu tuba, masu bauta, masu godiya ga Ubangijin mu". Muslim ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 28. Waccece addu'ar matafiyi ga mazauni?
Amsa: "Ina bawa Allah ajiyarku wanda abubuwan da aka baShi ajiya basa tozarta". Ahmad da Ibnu Majah ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 29. Mecece addu'ar mazauni ga matafiyi?
Amsa: "Ina bawa Allah ajiyar addinin ka, da amanar ka, da ƙarshen aikin ka". Ahmad da Tirmizi ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 30. Me cece addu'ar shiga kasuwa?
Amsa: "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah Shi kaɗai yake ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, kuma godiya tasa ce, Yana rayawa kuma Yana kashewa, Shi ne rayayye wanda ba ya mutuwa, dukkanin alhairai suna hannun Sa, kuma Shi Mai iko ne akan dukkan komai". Al-Tirmizi da Ibnu Majah ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 31. Ka faɗi addu'a yayin fushi?
"Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa". An haɗu akansa (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Tambayata 32. Me kake cewa ga wanda ya yi maka wani abin alheri?
Amsa; "Allah Ya saka maka da Alheri". Al-Tirmizi ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 33. Wacce addu'a ce idan abin hawa ya lalace?
Amsa: "Da sunan Allah". Abu Daud ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 34. Me kake cewa idan ka sami abinda yake faranta maka rai?
Amsa: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda da ni'amar Sa ne kyawawan ayyuka suke cika". Al-Hakim ne da wani suka ruwaito shi.
Tamabaya ta 35. Me kake cewa idan wani abinda ba ka so ya same ka?
Amsa: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah akowane irin hali". Sahihul Jam'i.
Tambaya ta 36. Mecece kaifiyyar yanda sallama take, da kuma amsa sallamar?
Amsa: Mutum musulmi yana cewa: "Amincin da rahamar Allah da kuma albarkar Sa su tabbata a gare ku".
Sai ɗan'uwansa ya mayar masa: "Ku ma amincin Allah da rahamar Sa da albarkar Sa su tabbata a gareku". A Tirmizi da Abu Dawud da kuma wanin su.
Tambaya ta 37. Wacce addu'a ake yi lokacin saukar ruwan sama?
"Ya Allah (ka sanya shi) mamakon ruwa mai amfani". Bukhari ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 38. Wacce addu'a ake yi bayan saukar ruwan sama?
Amsa: "An yi mana ruwa ne da falalar Allah da kuma rahamar Sa". Bukhari da Muslim.
Tambaya ta 39. Ka ambaci addu'ar iska (idan ta taso)?
Amsa: "Ya Allah ina roƙon Ka alherin ta, ina kuma neman tsarin Ka daga sharrin ta". Abu Dwud da Ibnu Majah.
Tambaya ta 40 Ka ambaci addu'ar (da ake yi ) yayin jin tsawa?
Amsa: "Tsarki ya tabbata ga wanda tsawa take tasbihi haɗi da gode maSa, Mal'iku kuma saboda tsoran Sa". Muwaɗɗa Malik.
Tambaya ta 41. Mecece addu'a idan ka ga wanda aka jarraba?
Amsa: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya bani lafiya daga abinda ya jarabe ka da shi, kuma ya fifita ni akan mafi yawan abinda ya halitta fifitawa". Al-Tirmizi ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 42. Addu'a ga wanda yaji tsoron kada ya samu wani abu da kambun bakan sa.
Amsa: (Ya zo) a Hadisi: "Idan ɗayan ku yaga abinda ya ƙayatar da shi daga ɗan'uwan sa, ko karan kan sa, ko a dukiyar sa, to ya yi addu'a ta samun albarka (Allah ya sanya albarka) domin lallai kambun baka gaskiya ne". Ahmad da Ibnu Majah da wasunsu ne suka ruwaito shi.
Tambaya ta 43. Yaya zaka yi salati ga Annabi - tsira da aminci su tabbata a gare shi?
Amsa: "Ya Allah! Ka yi daɗin tsira ga (Annabi) Muhammad da iyalan (Annabi) Muhammad, kamar yadda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da iyalan (Annabi) Ibrahim, lallai Kai abin godewa ne kuma Maigirma. Ya Allah! Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da iyalan (Annabi) Muhammad kamar yadda Ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da iyalan (Annabi) Ibrahim, lallai Kai abin godewa ne kuma maigirma". An haɗu akansa (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
BANKAGARAN ABUBUWA DABAN-DABAN21
Tambaya ta 1. Waɗanne hukunce-hukuncene guda biyar ta shari'a ta kallafa?
Amsa:
1- Wajibi.
2- Mustahabbi.
3. Haramun.
4. Makaruhi (Abin ƙi).
5. Halal.
Tambaya ta 2. Kayi bayanin waɗannan hukunce-hukuncen guda biyar?
Amsa:
1. Wajibi: Misalin, salloli biyar, da Azumin watan Ramadan, da biyayya ga iyaye.
- Shi wajibi ana ba wanda ya aikata shi lada, kuma ana yiwa wanda ya bar shi uƙuba.
2. Mustahabbi: Misalin, Nafilfili kafin salloli na farilla, da sallar dare, da ciyar da abin ci, da yin sallama, ana ambatan su da Sunnah da kuma Mandub.
- Shi Mustahabbi ana bawa wanda ya aikata shi lada, amma ba'a yiwa wanda ya bar shi uƙuba.
Babban abin lura:
Ya kamata ga musulmi alokacin da ya ji cewa wannan abun Sunna ne, ko Mustahabbi ne, to ya yi gaggawar aikata shi, da kuma koyi da Annabi - tsirada amincin Allah su tabbata a gare shi -.
3. Haramun: Kamar shan giya, da saɓawa iyaye, da yanke zumunci.
- Haram ana bada lada ga wanda ya bar shi, kuma ana yiwa wanda ya aikata shi uƙuba.
4. Makruhi: Kamar karɓa da bayarwa da hagu, naɗe tufafi a sallah.
- Shi abin ƙi, ana bada lada ga wanda ya bar shi, kuma ba'a yin uƙuba ga wanda ya aikata shi.
5. Halas: kamar cin tuffah, da shan shayi, ana ambaton sa: Ja'iz da Halal, (ma'ana: ya halatta).
- Shi halal, ba'a bada lada ga wanda ya bar shi, kuma ba'a yin uƙuba ga wanda ya aikata shi.
Tambaya ta 3. Menene hukuncin kasuwanci da sauran ma'amaloli?
Amsa: Asali dai akan abinda ya shafi dukkanin kasuwanci da sauran ma'amaloli halas ne, sai dai waɗansu nau'uka daga abinda Allah - maɗaukakin sarki - Ya haramta.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: "Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba". [Surat Al-Baƙara: 275].
Tambaya ta 4. Ka ambaci wasu daga cikin nau'ukan mu'amaloli da cinikin da aka haramta.
Amsa:
1. Algusu, dag cikin hakan akwai: Boye aibin haja (Abin sayarwa).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda dashi -, lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya wuce wani shuri - wato shuri - na abinci, sai ya shigar da hannunsa acikin sa, sai 'yan yatsun sa suka samu danshi, sai ya ce: " Menene wannan ya kai mai wannan abincin? Sai ya ce: Ai ruwan sama ne ya zuba acikin su ya Ma'aikin Allah, sai ya ce: "Shin ba ka sanya shi a saman abin cin ba, domin mutane su gan shi? Duk wanda ya yi mana algusu to baya tare da ni". Muslim ne ya ruwaito shi.
2. Riba: Daga cikinta in karɓi dubu ɗaya daga wani mutum bashi akan in dawo masa dasu da dubu biyu.
Karin, shi ne ribar da aka haramta.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce: "Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba". [Surat Al-Baƙara: 275].
3. Ruɗu da Jahilta: Kamar in siyar maka da madara a hantsar akuya, ko kuma kifi acikin ruwa, alhali ban kamo shi ba.
(Ya zo) acikin Hadisi: "Manzon Allah - tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi - yayi hani daga cinikin garari (Ruɗu). Muslim ne ya ruwaito shi.
Tambaya ta 5. Ka ambaci wasu daga cikin ni'imomin da Allah ya yi maka.
Amsa:1. Ni'imar Musulunci, kuma cewa kai baka zama daga ma'abota kafirci ba.
2. Ni'imar Sunnah, da cewa kai ba ka cikin 'yan bidi'a.
3. Ni'imar Lafiya, kamar ji da gani da tafiya, da sauran su.
4. Ni'imar abin ci, da abin sha, da kuma tufafi.
Ni'imomin sa - Maɗaukakin sarki - garemu masu yawa ne, bazasu ƙirbu ba, kuma ba za'a iya ƙididdige su ba.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce: {Kuma idan kun ƙidãya ni'imar Allah, bãza ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai}. [Surat Al-Nahl: 18].
Tambaya ta 6. Wanne wajibi (yake a kammu) ta waɗannan ni'imomin? kuma ta yaya zamu gode musu?
Amsa: Abinda yake wajibi: Shi ne gode musu, wannan ta hanyar yabo ga Allah, da gode maSa da harshe, da kuma cewa Shi ke da falala Shi kaɗai, da amfani da waɗannan ni'imomin ta abinda zai yardar da Allah - Maɗaukakin sarki -, ba ta hanyar saɓon Sa ba.
Tambaya ta 7. Waɗanne ne bukukuwan idi na Musulmai?
Amsa: Idin Karamar sallah, da kuma Idin Babbar sallah.
Kamar yadda ya zo acikin Hadisin Anas, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya gabato Madina, alhali su suna da kwanaki biyu da suke wasa a cikinsu, sai ya ce: "Waɗanne kwanaki biyu ne waɗannan?", sai suka ce: Mun kasance muna wasa a cikin su ne a lokacin Jahiliyya, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Haƙiƙa Ya canza muku su da waɗanda suka fisu alheri, su ne: Ranar Babbar Sallah, da kuma Ranar Karamar Sallah". Abu Dawud ne ya ruwaito shi.
Dukkan wasu bukukuwan idin da ba su ba, to suna daga cikin bidi'o'i.
Tambaya ta 8. Waɗanne watanni ne mafifa?
Amsa: Watan Ramdan.
Tambaya ta 9. Wace ranace mafificiya a kwanaki?
Amsa: Ranar Juma'a.
Tambaya ta 10. Wacce rana ce mafificiya acikin shekara?
Amsa: Ranar Arafah.
Tambaya ta 11. Wanne dare ne mafifici acikin shekara?
Amsa: Daren Lailatul Kadr.
Tambaya ta: 12. Wanne wajibi ne (a kanka) idan ka ga matar da ba taka ba?
Amsa: Wajibi shine rintse ido, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ka faɗawa muminai maza su rintse idanuwan su}. [Surat Al-Nur: 30].
Tambaya ta 13. Su waye maƙiyan mutum?
1. Rai mai umarni da mummnan aiki: Wannan shi ne mutum ya bi abinda ran shi yake riya masa da kuma san ran sa acikin saɓon Allah - mai girma da ɗaukaka -, tsarki ya tabbatar masa Ya ce: {Lalle rai mai umarnice da mummunan aiki, sai dai wanda Ubangijina Ya yi wa rahama, lalle Ubangiji na Mai yawan gafara ne kuma Mai yawan jinƙai ne}. [Surat Yusuf: 53]. 2. Shaiɗan. Shi ne maƙiyin ɗan Adam, babban manufarsa shi ne ya ɓatar da mutum, ya sanya masa waswasi na sharri, ya kuma shigar da shi wuta, Allah - Maɗaukakin sarki - ya ce: {Kuma kada ku bi hanyoyin shaiɗan, lallai cewa shi gareku maƙiyi ne mai bayyanar da ƙiyayya}. [Surat Al-Baƙarah: 168]. 3. Muggan abokai: Waɗanda suke kwaɗaitarwa akan sharri, kuma suna toshewa daga (aikata) alheri. Allah - Maɗaukakin sarki - yace: {Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne)}. [Surat Al-Zukhruf: 67].
Tambaya ta 14. Mecece tuba?
Amsa: Tuba: shi ne komawa daga saɓawa Allah - Maɗaukakin sarki - zuwa ga yi masa biyayya. Allah - Maɗaukain sarki - Ya ce: {Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa}. [Suratu Daha: 82}.
Tambaya ta 25. Menene sharuɗɗan tuba ingantattu?
Amsa: 1. Barin aikata zunubin.
2. Nadama akan abinda ya wuce.
3. Kudirin niyya akan ƙin kioma wa gareshi (aikata zunubi).
4. Mayar da haƙƙoƙi da abubuwa na zalinci ga masu su.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce: {Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sai su nẽmi gãfara ga zunubansu. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su nace a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa su suna sane}. [Surat Aal Imran: 135].
Tambaya ta 16. Menene Ma'anar salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -?
Amsa: Ma'anar sa shine cewa kai kana roƙon Allah da Yayi yabo ga Annabin Sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin taron jama'a maɗaukaka.
Tambaya ta 17. Menene ma'anar tsarki ya tabbata ga Allah?
Amsa: Tasbihi: Wato tsarkake Shi - tsarki ya tabbatar maSa ya ɗaukaka - daga dukkan wata tawaya da kuma aibi da mummuna.
Tambaya ta 18. Menene ma'anar Godiya ta tabbata ga Allah?
Amsa: Shine yabo ga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma siffanta Shi da dukkanin siffofi na kamala.
Tambaya ta 19. Menene ma'anar: Allah ne mafi girma?
Amsa: Wato cewa Shi tsarki ya tabbatar maSa Shi ne mafi girma daga dukkan komai, kuma mafi ɗaukaka, mafi girma mafi buwaya daga dukkan komai.
Tambaya ta 20. Menene ma'anar: Babu ƙarfi kuma babu dabara sai ga Allah?
Amsa: Ma'anar: Babu wani iya canjawa ga bawa daga wani hali zuwa wani halin, haka kuma babu wani ƙarfi akan hakan sai ga Allah.
Tambaya ta 21. Menene ma'anar: Ina neman gafarar Allah?
Amsa: Wato: Neman bawa daga Ubangijin Sa da Ya shafe masa masa zunuban sa, kuma Ya suturta aibobin sa.